Ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da tawagar ƙasar Sipaniya, Lamine Yamal, ya bayyana cewa dalilinsa na buga wasan ƙwallon ƙafa ya wuce batun neman kuɗi, yawan zira ƙwallaye, ko bayar da taimakon cin ƙwallo (assists), yana mai jaddada cewa yana buga wasan ne kawai don jin daɗinsa.
Jaridar Punch ta ruwaito daga wata tattaunawa da jaridar The Guardian ta yi da matashin ɗan wasan a ranar Asabar, inda ya ce ba ya son zama mai damuwa kan alkaluman nasararsa, yana mai bayanin cewa daɗin ƙwallon ƙafa na fitowa ne daga nuna ƙwarewa da kuma taimaka wa abokan wasa.
Yamal ya ce, “Ba na buga ƙwallo don kuɗi ba, ina bugawa ne saboda ina son wasan. ’Yan wasan da suka cika damuwa kan zira ƙwallaye ko bayar da taimakon cin ƙwallo ba sa jin daɗin wasan. Ni ina buga ƙwallo ne domin nishaɗi, yin dabarun yaudara da ƙwallo (dribble), buga ƙwallo ta taɓawa ɗaya ko biyu, da kuma sa abokin wasana da bai ci ba ya zura ƙwallo a raga, don samun farin ciki.”
Matashin ya kuma bayyana yadda suka yi da fitaccen ɗan wasan ƙasar Ajantina, Lionel Messi, inda ya ce ya je wurinsa ne kawai domin nuna masa godiya kan irin gudunmawar da ya bayar ga wasan ƙwallon ƙafa na duniya.
“Na je wajen Leo Messi na ce masa: na gode. Na gode masa sosai kan duk abubuwan da ya yi da kuma yadda yake a matsayin wanda ya fi kowa ƙwarewa. A koyaushe ina da yaƙinin cewa shi ne ƙwararre na farko,” in ji Yamal.
Yamal ya ƙara da cewa wannan haɗuwa ba shiri aka yi mata domin neman tallata kai a idon duniya ba, illa dai abin ya zo ne a dabi’ance lokacin da ya hango tauraron.
