Shugabannin jam’iyyar APC na wasu jihohin Nijeriya sun yi watsi kungiyar hadakar siyasa ta ‘Rainbow Coalition’ da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke jagoranta, inda suka buƙaci ya shiga jam’iyyar APC a hukumance idan yana son taimakawa wajen neman wa’adin biyu na Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Martanin shugabannin APC ya biyo bayan ƙarin samun saɓani tsakanin Wike da wasu gwamnonin jam’iyyar kan tsarin siyasar da yake ƙoƙarin ginawa gabanin babban zaɓen 2027, kamar yadda jaridar Pumch ta ruwaito.
Wike, wanda tsohon gwamnan jihar Rivers ne, yana riƙe da mukamin ministan Abuja a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, duk da cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP, wadda take adawa da APC.
Wike ya kafa Rainbow Coalition ne a matsayin wata ƙungiya mai ɗauke da ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban, inda ya ce manufarta ita ce tattara goyon baya ga Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, ba tare da tilasta wa ’yan siyasar su bar jam’iyyunsu ba.
Sai dai wasu shugabannin APC sun ce ba za su amince da tsarin da mutum zai goyi bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, yayin da a lokaci guda yake goyon bayan ’yan takarar wasu jam’iyyu a zaɓen gwamna da na majalisun tarayya ko jihohi ba.
Gwamnan jihar Zamfara kuma shugaban APC a matakin gwamnonin jam’iyyar, Dauda Lawal, ya ce dole Wike ya bayyana matsayinsa karara, ko dai ya shiga APC ko kuma ya ci gaba da tafiya da Rainbow Coalition.
Gwamna Lawal ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da aka gudanar a New York, inda ya ce matsayin gwamnonin APC kan batun bai sauya ba.
A cewar Lawal, ba za a iya kasancewa cikin wata jam’iyya ana aiki da ita, sannan a lokaci guda ana gina wata kungiyar siyasa da za ta goyi bayan wani ɓangare na APC ba.
Ya kuma bayyana cewa zai tattauna batun matsayin Wike da Shugaba Tinubu domin a samu cikakken bayani kan inda ministan yake a siyasar 2027.
A jihar Imo, sakataren yaɗa labarai na APC, Jones Onwuasoanya, ya buƙaci Wike ya shiga jam’iyyar a hukumance idan da gaske yake goyon bayan Tinubu.
Ya ce bai kamata mutum ya nuna goyon baya ga tsarin wata jam’iyya ba tare da kasancewa cikakken ɗan jam’iyyar ba, yana mai cewa APC a Imo ba ta amince da Rainbow Coalition a matsayin wata madadin tsarin siyasa ba.
A jihar Gombe ma, sakataren yaɗa labarai na APC, Murtala Usman, ya yi kira ga Wike da ya koma APC gaba ɗaya, yana mai cewa kafa Rainbow Coalition na iya haifar da rashin fahimta tsakanin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.
A jihar Ondo, sakataren APC, Alex Kalejaiye, ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta amince da tsarin da za a goyi bayan Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, yayin da ake goyon bayan ’yan takarar wasu jam’iyyu a sauran kujeru ba.
Ya ce manufar APC ita ce ta samu goyon bayan ’yan Nijeriya ga dukkan ’yan takararta, daga kujerar shugaban ƙasa zuwa majalisun tarayya da na jiha.
Sai dai APC ta jihar Jigawa ta nuna wani matsayi daban, inda sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Bashir Kundu, ya ce jam’iyyar ta yaba da goyon bayan da Wike ke bai wa Tinubu.
Kundu ya ce APC ta jihar Jigawa za ta marabci Wike idan ya yanke shawarar shiga jam’iyyar a hukumance, yana mai cewa kasancewar Wike na aiki wajen ganin Tinubu ya samu nasara ya isa a yaba masa.
A jihar Benue kuwa, martanin shugabannin APC an samu bambancin ra’ayi, inda wani ɓangare ya yaba da goyon bayan Wike ga Tinubu, yayin da wani ɓangaren ya ce zai fi so Wike ya shiga APC a hukumance.
A jihar Rivers, inda Wike ya taɓa zama gwamna, ɓangaren APC da Emeka Beke ke jagoranta ya goyi bayan matsayar wasu gwamnonin APC kan Rainbow Coalition.
Mai magana da yawun ɓangaren, Darlington Nwauju, ya ce bai dace Wike ya kasance a PDP a lokaci guda yana amfani da dangantakarsa da gwamnatin APC wajen gina wata sabuwar hanyar siyasa ba.
A jihar Anambra kuma, Shugaban APC na jihar, Sanata Emmanuel Anosike, ya soki shirin Rainbow Coalition, yana mai cewa Wike ba ɗan APC ba ne kuma bai kamata ya shiga cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar ba.
A jihar Kwara, Shugaban APC na jihar, Sunday Fagbemi, ya nuna shakku kan yadda tsarin Rainbow Coalition zai yi aiki, musamman ganin yadda zaɓen shugaban ƙasa, na majalisar dattawa da na wakilai ke gudana a lokaci guda.
Ya ce tsarin da zai sa mutum ya zaɓi jam’iyya ɗaya wajen shugaban ƙasa sannan wata jam’iyya a sauran kujeru na iya haifar da rudani ga masu kaɗa ƙuri’a, a cewar rahoton.
A jihar Plateau, Shugaban APC na jihar, Rufus Bature, ya ce jam’iyyar ba ta san da wata Rainbow Coalition a jihar ba, amma ya ce Wike yana da damar shiga APC idan yana son hakan.
A Nasarawa ma, sakataren yaɗa labarai na APC, Augustine Ogaba, ya yaba da goyon bayan Wike ga Tinubu, amma ya ce jam’iyyar za ta fi jin daɗi idan ministan ya shiga APC a hukumance.
Sai dai wasu jihohin sun ƙi bayyana matsaya kai tsaye, suna cewa batun ya fi ƙarfin matakin jiha kuma ya kamata shugabannin ƙasa na jam’iyyar su yanke hukunci a kai.
A Osun, mai magana da yawun APC, Kola Olabisi, ya ce batun ko Wike zai shiga APC ko a’a ya wuce matakin shugabancin jam’iyyar na jihar, yayin da APC ta Delta ta ce tana jiran matsayar shugabannin ƙasa.
A Bayelsa kuma, wani jigon APC, Doubara Joseph, ya buƙaci Wike ya shiga APC idan da gaske yake son taimakawa Tinubu, yayin da shugaban APC na jihar, Warman Ogoriba, ya ƙi yin tsokaci kan batun.
Wike, a nasa ɓangaren, ya ƙi amincewa da zargin cewa Rainbow Coalition wani tsarin APC ne ko kuma an kafa shi ne domin raunana jam’iyyar.
Ta bakin babban mataimakinsa na musamman kan yaɗa labarai Lere Olayinka, Wike ya ce ƙungiyar tana tattara goyon bayan Tinubu ne kawai a zaɓen shugaban ƙasa, yayin da ’yan siyasa ke da ’yancin zaɓar wanda za su goyi baya a sauran zaɓuka.
Wike ya kuma yi nuni da cewa irin wannan tsarin siyasa ya taɓa faruwa kafin zaɓen 2023, lokacin da shi da wasu ’yan G5 suka goyi bayan Tinubu ba tare da sun fice daga PDP zuwa APC ba.
Ministan ya kuma jaddada cewa “siyasa ta gida ce”, wato ’yan siyasa a kowace jiha suna da damar tsara yadda za su yi kawance da sauran ’yan siyasa bisa la’akari da yanayin siyasar jiharsu.
Wannan rikici ya ƙara nuna bambancin ra’ayi tsakanin Wike da wasu shugabannin APC kan yadda ya kamata a tsara goyon bayan Tinubu a 2027, da kuma irin rawar da tsarin jam’iyyar zai taka wajen wannan goyon baya.
