DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 29, 2026
HomeBabban Labari Talakawa ne suka fi shan wahala a ƙasar da cin hanci ya...

Talakawa ne suka fi shan wahala a ƙasar da cin hanci ya yi mata dabaibayi – Obasanjo

Tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce cin hanci da rashawa da kuma dukiyar da ba a bayyana tushenta ba na kawo cikas ga ci gaban ƙasa, yana mai cewa talakawa ne suka fi shan wahala a al’ummar da cin hanci ya yi mata yawa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Obasanjo ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Legas, yayin da yake jagorantar taron ƙaddamar da wani littafi wanda babban Lauyan Nijeriya, Dr Wahab Shittu, SAN, ya rubuta.

Taron ƙaddamar da littafin ya gudana ne a Oriental Hotel da ke Victoria Island, Legas, inda aka tattauna kan dokoki da hanyoyin da za su taimaka wajen gano dukiyar da ba a bayyana tushenta ba da kuma yaƙi da haramtacciyar dukiya.

Obasanjo ya ce cin hanci da rashawa ba ya dacewa da ci gaba, yana mai cewa duk yadda aka kira shi, yana cutar da al’umma kuma yana kawo cikas ga ci gaban ƙasa.

Ya bayyana cewa sha’awarsa ta yaƙi da cin hanci ta samo asali tun lokacin da yake aikin soja, lokacin da ya taɓa aiki a matsayin mai gabatar da ƙara ƙarƙashin dokokin soja tare da shiga kotun soji da ta duba wasu batutuwan da suka shafi cin hanci.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce bayan ya bar aikin soja ya koma aikin gona, tsohon jami’in bankin duniya kuma wanda ya kafa Transparency International, Peter Eigen, ya tuntuɓe shi domin su haɗa kai wajen yaƙi da cin hanci a duniya.

A cewar Obasanjo, Eigen ya shaida masa cewa abubuwan da ya gani yayin aikinsa a bankin duniya sun nuna yadda ake karkatar da wasu kuɗaɗen rance da ƙasashe ke karɓa, lamarin da ya ƙara masa ƙwarin gwiwar shiga yaƙi da cin hanci.

Ya ce daga bisani shi da Eigen suka kafa ƙungiyar Transparency International, inda Obasanjo ya zama shugaban kwamitin ba da shawara na ƙungiyar, yayin da Eigen ya zama shugabanta.

Obasanjo ya kuma tuna cewa lokacin da suka nemi goyon bayan tsohon shugaban bankin Duniya, Robert McNamara, ya gaya musu cewa suna ƙoƙarin yin abin da ke da matuƙar wahala.

Sai dai ya ce McNamara daga baya ya yi alkawarin ba su tallafin kuɗi idan suka samu damar nuna sakamakon ayyukansu.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce shi da Eigen sun zagaya ƙasashe daban-daban a Latin Amurka, Asiya da Afirka domin neman goyon baya ga yaƙin da suke yi da cin hanci.

Ya ce ɗaya daga cikin matakan farko da suka ɗauka shi ne matsa wa kungiyar haɗin kan tattalin arziƙi da ci gaba (OECD) lamba kan batun bai wa kamfanoni damar cire kuɗaɗen rashawa da suka biya a matsayin kuɗin haraji.

Obasanjo ya ce ya ɗauki kusan shekaru uku kafin OECD ta dakatar da wannan tsarin, lamarin da ya taimaka wajen ƙara wa Transparency International karɓuwa a duniya.

Ya kuma bayyana irin rawar da gwamnatinsa ta taka wajen kafa hukumar yaƙi da cin hanci da sauran laifukan da suka shafi hakan (ICPC) a Nijeriya.

A cewarsa, Transparency International ta ba shi wani samfurin dokar yaƙi da cin hanci, wanda daga baya ya zama tushen dokar da ta kafa ICPC a Nijeriya.

Obasanjo ya ce dokar ta fuskanci turjiya a majalisar kasa, inda wasu ’yan majalisa suka nuna fargabar cewa idan aka amince da ita yadda take, za ta iya jefa wasu daga cikinsu cikin matsala.

Ya ce daga ƙarshe an shafe kusan watanni 18 ana aiki kafin a kammala amincewa da dokar, sannan daga baya ya kafa hukumar yaƙi da masu yi Wa tattalin arziƙi zagon kasa wato (EFCC) domin ƙara ƙarfafa yaƙi da cin hanci da laifukan kuɗi.

Obasanjo ya kuma yaba wa tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu, bisa rawar da ya ce ya taka wajen yaƙi da cin hanci tun farkon kafuwar hukumar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata