Ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziƙi, Atiku Bagudu, ya ce Nijeriya na da ɗaya daga cikin kasashe mafi ƙanƙantar kasafin kuɗi idan aka kwatanta da sauran ƙasashe 10 da suka fi yawan al’umma a duniya, duk da yawan jama’a da kuma buƙatun ci gaban ƙasar.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja, yayin wani taron horas da jami’an yaɗa labarai na Majalisar Dattawa, wanda aka shirya kan yadda za a yi amfani da sa ido da haɗin gwiwar kafafen yaɗa labarai wajen kare kasafin kuɗin ƙasa daga shigar da abubuwan da ba su dace ba.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Bagudu ya yi kira da a fara wata tattaunawa ta ƙasa kan yadda za a ƙara kuɗaɗen shiga da kuma faɗaɗa damar gwamnati ta samun kuɗin gudanar da ayyukan raya ƙasa.
Ya ce ya kamata tattaunawar kasafin kuɗin Nijeriya ta fara ne da tambaya kan abin da ake nufi da kasafin kuɗin ƙasa da kuma irin girman kasafin da ya dace da yawan jama’a da buƙatun ci gaban ƙasar.
A cewar ministan, ƙarancin kuɗaɗen da gwamnati ke da damar kashewa idan aka kwatanta da yawan jama’a da buƙatun ci gaba na haifar da tambayar ko matakin kashe kuɗin gwamnati a yanzu ya isa cimma manufofin ci gaban Nijeriya.
Bagudu ya ce daga cikin ƙasashe 10 da suka fi yawan jama’a a duniya, Nijeriya ce ke da mafi ƙanƙantar kasafin kuɗi, yana mai cewa ya kamata a tattauna kan yadda za a ƙara samar da kuɗaɗen shiga.
Ya kuma bukaci ’yan jarida da su riƙa yin tambayoyi masu ma’ana tare da zurfafa bincike kan abubuwan da ke cikin kasafin kuɗi, maimakon yanke hukunci ba tare da cikakken bayani ba.
Ministan ya ce sa ido kan kasafin kuɗi bai kamata ya tsaya kawai wajen gano abubuwan da ake ganin suna da cece-kuce ba, sai dai ya kamata a binciki asalin kowanne tanadi, dalilin da ya sa aka sanya shi da kuma irin buƙatar ci gaban da aka tsara zai magance.
Bagudu ya danganta batun da ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Tinubu da kuma burin gwamnati na gina tattalin arzikin da zai samar da ƙarin wadata da dama ga jama’a.
Ya ce Agenda 2050 ma na cikin manyan tsare-tsaren da ya kamata a yi la’akari da su yayin yanke shawarar yadda za a tara kuɗaɗen shiga da kuma inda za a mayar da kuɗaɗen gwamnati.
Ministan ya kuma ce burin Nijeriya na gina tattalin arzikin da darajarsa za ta kai dala tiriliyan ɗaya na buƙatar ƙasar ta fuskanci tambayoyi masu muhimmanci kan yadda za ta tara kuɗaɗe da kuma yadda za ta ɗauki nauyin ayyukan raya ƙasa.
A cewarsa, batutuwan kuɗaɗen shiga, kashe kuɗi da kuma karɓar bashi suna da alaƙa da amincewar jama’a, saboda fahimtar ’yan Nijeriya da kuma goyon bayansu na da muhimmanci wajen aiwatar da manyan matakan tattalin arziki.
Bagudu ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da majalisar kasa ke takawa wajen tsara da kuma amincewa da kasafin kuɗin ƙasa, yana mai cewa kundin tsarin mulki ya ba majalisa muhimmiyar damar shiga cikin tsarin kasafin kuɗi.
Saboda haka, ya yi kira da a ƙara wayar da kan jama’a kan dangantakar da ke tsakanin ɓangaren zartarwa da majalisa wajen tsara kasafin kuɗin ƙasa.
Dangane da zargin shigar da wasu abubuwa cikin kasafin kuɗi ba bisa ƙa’ida ba, ministan ya gargadi ’yan jarida da kada su ɗauka cewa duk wani tanadi da ba su saba gani ba lallai ne ya kasance ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ce ya kamata a binciki asalin tanadin, manufarsa da kuma waɗanda ake sa ran za su amfana kafin a yi masa hukunci.
Bagudu ya ce kuskuren ɗan Adam na iya faruwa a cikin tsarin gudanar da ayyukan gwamnati, don haka ya kamata kafafen yaɗa labarai da majalisa su ci gaba da yin taka-tsantsan wajen sa ido kan yadda ake tafiyar da kasafin kuɗi.
Ya kuma yi kira da a samu daidaito tsakanin buƙatar gwamnati ta kasance mai gaskiya da buɗe bayanai da kuma kare wasu bayanai masu muhimmanci da suka shafi tsaron ƙasa ko wasu muhimman muradun ƙasa.
A cewarsa, ’yan jarida na da muhimmiyar rawa wajen riƙe hukumomin gwamnati da alhaki, amma ya kamata rahotannin kasafin kuɗi su riƙa la’akari da manyan ƙalubalen ci gaban Nijeriya.
Bayanan wani bincike da Punch ta wallafa a watan Agusta sun nuna cewa jimillar kasafin kuɗaɗen jihohi 36 na Nijeriya da babban birnin tarayya Abuja ta ƙaru da kashi 47.5 cikin 100, daga Naira tiriliyan 27.22 a shekarar 2025 zuwa Naira tiriliyan 40.14 a shekarar 2026.
Sai dai duk da wannan ƙarin, kaso na kuɗaɗen da aka ware domin ayyukan manyan gine-gine ya ragu daga kashi 73.24 cikin 100 a shekarar 2025 zuwa kashi 64.34 cikin 100 a shekarar 2026.
A zahiri kuwa, adadin kuɗin da aka ware wa ayyukan raya ƙasa ya ƙaru daga Naira tiriliyan 19.94 zuwa Naira tiriliyan 25.83, abin da ke nuna cewa abin da ya ragu shi ne kaso daga cikin jimillar kashe kuɗin, ba adadin kuɗin da aka ware ba.
