Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alkawarin cewa zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a zaɓen 2027, bayan ya ce gwamnatinsa za ta magance matsalar cin hanci da rashawa a ƙasar.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Obi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wani taron tattaunawa da aka shirya domin ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa na NDC, Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, a birnin Sokoto.
Tsohon Gwamnan jihar Anambra ya ce matsalar cin hanci da rashawa ce babbar ƙalubalen da ke addabar Nijeriya, yana mai cewa idan aka magance ta, za a samu damar sake duba tsarin tallafin man fetur.
Obi ya ce ana yawan magana kan batun tallafin man fetur, amma a ganinsa, babban abin da ya kamata a fara magancewa shi ne cin hanci da rashawa da yake da alaƙa da harkokin man fetur da sauran sassan tattalin arzikin ƙasa.
Ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta ɗauki matakan da suka dace domin dakile cin hanci da rashawa a dukkan ɓangarorin gwamnati.
A cewarsa, magance cin hanci zai taimaka wajen samar da yanayin da za a iya amfani da dukiyar ƙasar wajen inganta rayuwar jama’a.
Obi ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su yi amfani da zaɓen 2027 wajen zaɓar ’yan takarar NDC a matakai daban-daban, yana mai cewa hakan zai kasance wani ɓangare na ƙoƙarin magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
Ya ce jam’iyyarsa tana son kafa abin da ya kira “siyasar kulawa da hidima ga ’yan Nijeriya”, wadda za ta mayar da hankali kan bukatun jama’a.
Dan takarar ya kuma nuna damuwa kan halin da tattalin arzikin ’yan Nijeriya ke ciki, yana mai cewa idan aka ba shi damar jagorantar ƙasar, zai mayar da hankali wajen amfani da albarkatun Nijeriya domin inganta tsaro, ilimi da sauran muhimman sassan tattalin arziki.
Obi ya bayyana cewa ilimi ne zai kasance babban abin da gwamnatinsa za ta ba muhimmanci bayan haɗin kan ƙasa da tsaro, yana mai jaddada muhimmancin ilimi wajen ci gaban al’umma.
Haka kuma, ya yi alkawarin haɗa manyan biranen jihohin Nijeriya da layin dogo domin sauƙaƙa harkokin kasuwanci da zirga-zirga tare da bunƙasa tattalin arziki.
A nasa ɓangaren, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ziyarar Sokoto ta kasance wani ɓangare na ganawa da al’umma da neman goyon bayansu gabanin zaɓen 2027.
Tsohon Gwamnan jihar Kano ya ce kafin taron sun ziyarci Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar, inda ya yi musu addu’a tare da isar da fatan alheri ga tikitin Obi da Kwankwaso.
Kwankwaso ya kuma bayyana cewa yankin Arewa maso Yamma na daga cikin wuraren da matsalar ’yan bindiga da garkuwa da mutane ta fi tsananta, yana mai cewa NDC na da burin tunkarar waɗannan ƙalubale idan aka ba ta damar jagorantar ƙasar.
A nasa ɓangaren, ɗan takarar gwamnan Sokoto na NDC, Dakta Shamsudeen Haido, ya yi alkawarin samar da shugabanci nagari idan aka zaɓe shi a zaɓen 2027.
Shi kuwa shugaban NDC na jihar Sokoto, Bello Yabo, ya ce taron ya ba mazauna jihar damar jin kai tsaye daga Obi da Kwankwaso kan tsare-tsarensu da hangen nesansu game da makomar Nijeriya.
