DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 29, 2026
HomeBabban Labari Talauci zai ƙara ta’azzara a Arewa idan Tinubu ya sha kaye a...

Talauci zai ƙara ta’azzara a Arewa idan Tinubu ya sha kaye a 2027 – APC

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi gargadin cewa talauci zai iya ƙara ta’azzara a yankin Arewa tare da samun koma baya a wasu ayyukan ci gaba idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai samu wa’adi na biyu a zaɓen 2027 ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Yilwatda ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake karɓar wasu tsoffin ’yan jam’iyyar ADC, da suka sauya sheƙa zuwa APC ƙarƙashin jagorancin Aslam Aliyu.

Shugaban APC ya ce wasu daga cikin tsare-tsaren gwamnatin Tinubu, ciki har da ayyukan gina tituna, tallafin rance ga ɗalibai, shirin amfani da iskar gas ɗin CNG da kuma matakan da suka shafi samar da takin zamani, sun taimaka wa jihohin Arewa.

A cewarsa, yankin Arewa ba zai iya komawa ga yanayin tattalin arzikin da ake ciki kafin zuwan gwamnatin Tinubu ba, musamman matsalolin da gwamnatocin jihohi ke fuskanta wajen biyan albashi da fansho.

Yilwatda ya kuma soki shirin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar na dawo da tallafin man fetur, yana tambayar yadda za a samar da kuɗin gudanar da irin wannan tsari ba tare da rage wasu shirye-shiryen gwamnati ba.

Ya ce cire tallafin man fetur ya bai wa gwamnatin tarayya damar samun ƙarin kuɗaɗen da take amfani da su wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen tallafa wa jama’a.

Shugaban APC ya ce idan aka dawo da tallafin man fetur, hakan na iya shafar kuɗaɗen da ake warewa ayyukan more rayuwa, musamman gina tituna a sassan ƙasar.

Ya kuma tambayi ko shirye-shiryen rage tsadar sufuri da inganta samar da makamashi za su ci gaba idan aka sauya tsarin da ake bi a halin yanzu.

A cewarsa, manufofin gwamnati da suka shafi iskar gas da takin zamani na da muhimmanci ga manoma da tattalin arzikin yankin Arewa, saboda noma na daga cikin manyan hanyoyin samun abin rayuwa a yankin.

Yilwatda ya kuma ambaci shirin CNG, yana mai cewa gwamnatin tarayya na amfani da shi a matsayin wani ɓangare na matakan rage nauyin tsadar sufuri da ke kan jama’a masu ƙaramin ƙarfi.

Game da ilimi kuwa, shugaban APC ya ce ɗalibai daga yankin Arewa na daga cikin masu cin gajiyar shirin Nigerian Education Loan Fund (NELFUND), wanda ke bai wa ɗalibai damar samun rancen biyan kuɗaɗen karatu.

Ya yi tambayar abin da zai faru da ɗaliban da ba su da damar biyan kuɗin makaranta da kansu idan aka dakatar da irin wannan shiri.

Yilwatda ya kuma yi magana kan halin kuɗaɗen jihohin Arewa kafin Shugaba Tinubu ya hau mulki, yana mai cewa akwai jihohi da dama da suka fuskanci matsalar rashin iya biyan albashi da sauran hakkokin ma’aikata.

Ya yi ikirarin cewa daga cikin kusan jihohi 30 da ya ce ba su iya biyan albashi a wancan lokaci, duk jihohin Arewa suna cikin matsalar.

Ya ce bai kamata a koma ga irin wannan yanayi ba, yana mai cewa rashin biyan albashi da alawus-alawus na iya ƙara matsin tattalin arziki da talauci a yankin.

Shugaban APC ya ƙara da cewa ƙalubalen talauci da matsin tattalin arziki ba su tsaya ga Arewa kaɗai ba, sai dai ya ce wasu matakan gwamnatin tarayya sun taimaka wajen rage wasu matsalolin da jihohi da gidaje ke fuskanta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata