DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 2, 2026
HomeBabban Labari Manufofin haraji na gwamnatin Tinubu na bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya - Adedeji

Manufofin haraji na gwamnatin Tinubu na bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya – Adedeji

Shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta Nijeriya (NRS), Dr Zacch Adedeji, ya ce sauye-sauyen da hukumar ke aiwatarwa a tsarin haraji na da nufin tallafa wa ’yan kasuwa da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Adedeji ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin bikin baje kolin kasuwanci na Abuja karo na 21, wanda ƙungiyar ’yan kasuwa ta Abuja (ACCI) ta shirya da taken “ƙarfafa tattalin arziki, ciniki, da haraji”.

Ya ce taken taron ya zo a kan lokaci, yana mai jaddada muhimmancin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin bunƙasa tattalin arziki.

A cewarsa, sauye-sauyen harajin sun mayar da hankali ne wajen sauƙaƙa tsarin haraji, tabbatar da adalci da gaskiya, tare da rage wahalhalun da ’yan kasuwa ke fuskanta wajen biyan haraji.

Adedeji ya ce amfani da fasaha ta hanyar manhajoji kamar Rev360 da tsarin aika takardun biyan haraji ta yanar gizo zai sauƙaƙa rajista, cike bayanan haraji da biyan kuɗaɗen haraji.

Ya kuma buƙaci ’yan kasuwa su riƙa tuntubar hukumar domin bayyana ƙalubalen da suke fuskanta, yana mai cewa NRS za ta ci gaba da sauraron su, da inganta tsarin aiki da rage hanyoyin zurarewar kuɗaɗen shiga.

A nasa ɓangaren, mataimakin shugaban na biyu a hukumar, Dr Aliyu Hong, da babban daraktan ƙungiyar, Agbaidu Jideani, sun jaddada muhimmancin ci gaba da tattaunawa tsakanin hukumar haraji da ’yan kasuwa domin samar da yanayin kasuwanci mai sauƙi, tabbatacce da zai ƙarfafa saka jari da samar da ayyukan yi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata