DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeLabaraiNELFund sun musanta karkatar da kudaden bashin karatun dalibai 

NELFund sun musanta karkatar da kudaden bashin karatun dalibai 

Shirin ba da bashin karatu na Najeriya NELFund ya musanta zargin karkatar da kudaden da aka bai wa dalibai.

Wannan dai na zuwa ne bayan da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta ce tana gudanar da bincike kan zargin almundahana a yayin raba kudaden.

A cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na asusun, Oseyemi Oluwatuyi, NELFund ya fitar, ya ce an yi wa kalaman ICPC gurguwar fahimta ne.

A gefe guda hukumar ta ICPC ta yi karin haske kan bayanin da ta yi a baya game da bashin karatun daliban.

Mai magana da yawun hukumar, Demola Bakare, ya ce hukumar za ta yi bincike kan yadda aka kashe kudade ne da suka kai biliyan 100 saboda bayanan da ta samu cewa makarantu 51 sun karkatar da kudaden ba bisa ka’ida ba.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata