Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi watsi da zargin da tsohon gwamnan jihar Elrufa’i ya yi, na cewa gwamnatinsa da kuma ta tarayya na biyan ‘yan bindiga a sassa daban-daban na Najeriya domin dakatar da ayyukan su.
Gwamnan yayi wannan jawabi ne a tattaunawar sa cikin shirin siyasar gidan talabijin na TVC, yana mai bayyana zargin a matsayin abin da bai dace ba a siyasance, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A baya dai yayin hirar sa da gidan talabijin na Channels, Elrufa’i ya soki matakin da gwamnati ke dauka na yin sulhu da ‘yan bindiga a wasu yankunan Najeriya, lamarin da ya nuna rashin goyon bayan sa, domin kuwa a cewar sa, gwamnati karfafa musu gwiwa kawai take yi.
Sai dai Uba Sani ya ce gwamnatinsa ba ta bayar da kudi ga’ yan bindiga ba, amma za ta ci gaba da kokarin kawo karshen ayyukan ta’addanci ta hanyoyin da suka dace.
