Jam’iyyar ADC ta sanar da cewa ta yi nasarar loda sunaye da bayanan ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da mataimakinsa, Rotimi Amaechi, a shafin karɓar sunayen ’yan takara na Hukumar Zaɓe ta Nijeriya (INEC).
Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a daren Talata.
Abdullahi ya ce matakin wani muhimmin ci gaba ne a shirye-shiryen jam’iyyar gabanin babban zaɓen ƙasa.
Ya ƙara da cewa loda sunayen ’yan takarar na nuna ƙudirin ADC na bai wa ’yan Nijeriya wata madaidaiciyar hanya da ta ginu kan ƙwarewa, haɗin kai da kuma farfaɗo da ƙasa.
