DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeBabban Labari Shugaba Tinubu ya bayyana dalilin yin garambawul a shirin NYSC

Shugaba Tinubu ya bayyana dalilin yin garambawul a shirin NYSC

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa garambawul da gwamnatinsa ta yi wa shirin bautar ƙasa na NYSC na da nufin bai wa matasan Nijeriya ƙwarewar aiki da kuma shirya su domin taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ƙasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, bayan Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da sauye-sauyen a ranar Litinin.

Ya ce sauye-sauyen na daga cikin alƙawarin da ya yi lokacin da ya hau mulki na samar wa matasa damammaki da za su inganta rayuwarsu.

Shugaban ya ce duk da cewa NYSC ta taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa tun bayan kafuwarta a shekarar 1973, lokaci ya yi da za a daidaita tsarin da bukatun Nijeriya ta yau.

A cewarsa, matasa kusan kashi 70 cikin 100 na al’ummar Nijeriya ne, don haka ya kamata a ɗauke su a matsayin ginshiƙin ci gaban ƙasa ba nauyi ba.

Sabon tsarin ya tanadi tsawaita lokacin sansanin NYSC daga makonni uku zuwa makonni shida, inda za a ƙara horo kan shugabanci, kishin ƙasa, sana’o’i, ilimin fasahar zamani da harkokin kuɗi.

Haka kuma za a ba masu yi wa ƙasa hidima horo bisa fannin karatunsu da burinsu na sana’a, ciki har da noma, lafiya, ilimi, fasaha, shari’a, harkokin gwamnati, kasuwanci da tsaro.

Tinubu ya kuma ce za a inganta tsarin tura masu bautar ƙasa ta hanyar amfani da fasaha, tare da la’akari da yanayin tsaro da kuma bai wa ’yan asalin jihohi, mazauna jihohi da waɗanda suka yi karatu a wuraren da ake da matsalar tsaro fifiko.

Ya ƙara da cewa sabon tsarin zai sauya shugabancin NYSC, inda farar hula za ta jagoranci hukumar a matsayin Darakta Janar, tare da wasu manyan daraktoci uku, ciki har da jami’in tsaro daga soja ko wata hukumar tsaro.

Tinubu ya umarci Ma’aikatar Matasa da Ma’aikatar Shari’a da su fara aikin gyaran dokar NYSC domin bai wa waɗannan sauye-sauye cikakken matsayi a doka, yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da gina Nijeriya da za ta bai wa matasa damar cimma burinsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata