Sabbin bayanai daga dandalin sa ido kan kashe kudaden gwamnati na Govspend sun nuna cewa wasu hukumomin gwamnatin Nijeriya biyu sun kashe jimillar naira biliyan 25.9 cikin rana guda, yayin da aka gano wasu ma’amaloli na kudi na kusan naira biliyan 2.85 da ake zargin maimaitattu ne.
Rahoton da Daily Trust ta bincika ya nuna cewa mafi yawan kudaden an kashe su ne a ranar 31 ga Maris, 2026, ta hannun Federal Co-operative College da ke Oji River a jihar Enugu da kuma Federal College of Horticulture da ke Dadin-Kowa a jihar Gombe.
Binciken ya nuna cewa wasu daga cikin ayyukan da aka biya kudinsu ba su da alaka kai tsaye da ayyukan hukumomin biyu kamar yadda dokokinsu suka tanada.
Mafi daukar hankali a cikin bayanan shi ne yadda aka maimaita biyan kudi naira miliyan 268.4 sau takwas domin ayyukan hanyoyi da magance kwararar ruwa a yankuna daban-daban.
Kamfanoni takwas daban-daban sun karbi wannan adadi iri daya tare da kusan bayanin aiki iri daya daga Federal Co-operative College, Oji River.
Kamfanin Swam Construction Ltd ya samu naira miliyan 268.4 domin aikin hanyoyi da magance ambaliyar ruwa a yankin Uzii, yayin da Gorrion Engineering Ltd shi ma ya samu irin wannan kudi domin aikin hanya mai tsawon kilomita daya da magudanan ruwa a Eziama.
Sauran kamfanonin da suka samu irin wannan adadi sun hada da Diamond Leeds Ltd, Ice Target Project Ltd, Hard Harts Construction Ltd, Zentrum Builders Ltd, Gold Reef Construction Ltd da Alpin Leeds Construction Ltd.
Jimillar wadannan ma’amaloli takwas ta kai naira biliyan 2.14, wanda ya zama mafi girman bangare na kudaden da aka yi wa alama a matsayin maimaitattu.
Bugu da kari, kwalejin ta sake fitar da wasu kudade guda 17 na naira miliyan 29.1 kowanne a rana guda domin ayyukan da suka shafi mazabun ‘yan majalisa a jihohi daban-daban.
Kamfanonin da suka ci gajiyar wadannan kudade sun hada da Stargate Global Resources Mega Concepts Ltd domin kayan feshi na koko a Cross River da Heartland Associates Ltd domin kayan abinci a Lagos.
Haka kuma an biya wasu kamfanoni kudade iri daya domin kayan noma, taki, kayan makaranta, fitilun hasken rana da sauran ayyuka a jihohin Kogi, Kano, Ogun, Rivers, Katsina, Osun da Anambra.
Rahoton ya kuma nuna cewa Federal College of Horticulture da ke Dadin-Kowa ta kashe naira miliyan 845.8 a rana guda ga wasu kamfanoni uku domin ayyukan da ba su da alaka kai tsaye da koyarwar noma da binciken kimiyya.
Wadannan bayanai sun kara jawo hankalin jama’a kan yadda ake tafiyar da kudaden gwamnati, musamman yadda ake gudanar da ayyukan da suka shafi mazabu da kuma bin dokokin kashe kudaden gwamnati.
