DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 20, 2026
HomeSiyasaPDP tsagin Turaki za ta tantance ‘yan takara sama da 3,000 a...

PDP tsagin Turaki za ta tantance ‘yan takara sama da 3,000 a matakai daban-daban

Tsagin jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki ya bayyana cewa za a tantance ‘yan takara 3,181 domin neman mukamai daban-daban kafin babban zaben 2027.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce adadin ya kunshi masu neman takarar shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci, ‘yan majalisar wakilai da kuma ‘yan majalisun jihohi.

A cewar jam’iyyar, mutum 2,122 ne suka nemi tikitin kujerun majalisun jihohi, yayin da mutum 748 suka nemi tikitin majalisar wakilai.

Hakazalika, mutum 198 ne suka nemi tikitin kujerar sanatoci, yayin da mutum 112 suka nemi takarar gwamna.

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa mutum daya ne kacal ya nemi tikitin takarar shugaban kasa a karkashin tsagin.

PDP ta sanar da hakan ne tare da bayyana sunayen kwamitocin tantance ‘yan takara da kuma kwamitocin sauraron korafe-korafe.

Wani bangare na sanarwar ya ce an kafa kwamitocin ne bisa jadawalin ayyuka da kwamitin zartarwa na kasa na jam’iyyar ya amince da shi domin shirye-shiryen babban zaben 2027.

Sanarwar ta kara da cewa matakin ya yi daidai da dokoki da tsarin jam’iyyar na gudanar da zabubbukan cikin gida cikin adalci da gaskiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata