Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC, Farfesa Joash Amupitan, da yin amfani da mukaminsa wajen haddasa rikici a cikin jam’iyyun adawa domin raunana su gabanin zaɓen shekarar 2027.
Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar a madadinsa ranar Litinin, inda ya ce abin da INEC ta yi game da rikicin shugabancin jam’iyyar ADC ya nuna son kai da kuma rashin bin ƙa’ida.
A cewarsa, zargin ya biyo bayan ikirarin Nafiu Bala Gombe, wanda ke kiran kansa shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, cewa ya samu nasarar sanya sunayen ’yan takarar jam’iyyar a shafin INEC na yanar gizo domin shirye-shiryen zaɓen 2027.
Atiku ya ce ɗoara sunayen ’yan takara a shafin INEC na daga cikin matakan shirye-shiryen zaɓe, wanda ake yi ne bayan hukumar ta bai wa jam’iyyu lambobin shiga yanar gizonta, amma ya yi zargin cewa bai kamata a bai wa Nafiu Bala Gombe wannan damar ba.
Ya ce INEC ta riga ta amince da Sanata David Mark a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar ADC, don haka bai dace a bai wa wani da ba a amince da shi ba damar gudanar da harkokin jam’iyyar ba.
Atiku ya bayyana cewa idan har INEC ta bai wa bangarorin biyu lambobin shiga, hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa da kuma dokokin zaɓe, kuma zai iya jefa jam’iyyar ADC cikin sabon rikici.
Ya kuma yi zargin cewa wannan ba shi ne karo na farko da INEC ƙarƙashin jagorancin Farfesa Joash Amupitan ke nuna son kai ba, yana mai cewa hukumar ta taba cire sunayen halastattun shugabannin ADC daga bayananta duk da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.
Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya jaddada cewa duk wani ɗan takara da ba ya fito daga tsarin shugabancin da Sanata David Mark ke jagoranta ba, ba shi da inganci a doka, domin bai fito ta hanyar sahihin zaɓen fidda gwani ba.
Atiku ya buƙaci INEC da ta guji duk wani mataki da zai haddasa rikici a cikin jam’iyyun siyasa, yana mai cewa ya kamata hukumar ta kasance mai zaman kanta da adalci ga kowa.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumar INEC ba ta fitar da wata sanarwa ko martani kan zarge-zargen da Atiku Abubakar ya yi ba.
