An rantsar da Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.
Wakilin DCL Hausa, Sadiq Muhammad Fagge, ya ruwaito cewa Murtala Garo, tsohon dan takarar mataimakin gwamnan Kano a zaben 2023, ya sha rantsuwar ne yayin wani taro da ya gudana a fadar gwamnati a yau Talata.
Wannan ya kawo karshen shafe makonni cikin rashin tabbas kan wanda zai maye gurbin Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo, wanda yayi murabus bayan sakamakon raba hanya a siyasa.
Kafin wannan lokaci dai, Gwamna Abba ya aike da sunan Murtala da Gwamna Abba ga majalisar dokokin Kano domin tantance shi a matsayin mataimakinsa.
Kamar yadda rahotanni da kuma majiyoyi suka nuna, an zabo Murtala Sule Garo ne, biyo bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC.
A yayin rantsuwar, an hangi fuskokin wasu jiga-jigai a cikin jam’iyyar APC irin su Abdullahi Umar Ganduje, Malam Ibrahim Shekarau, Sanata Barau Jibrin da sauran manyan ‘yan siyasa.
