DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeSiyasaTinubu ya taya Murtala Garo murnar zama mataimakin Gwamnan Kano

Tinubu ya taya Murtala Garo murnar zama mataimakin Gwamnan Kano

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya taya Murtala Sule Garo murna bisa zama sabon mataimakin Gwamnan Jihar Kano, bayan rantsar da shi da aka yi a ranar Talata.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Garo domin cike gurbin kujerar sakamakon murabus ɗin Aminu Abdulsalam Gwarzo, wanda ya ajiye mukaminsa bayan sauya sheƙar Gwamnan zuwa jam’iyyar APC.

Dan siyasar mai shekaru 48 ya taɓa rike mukamai daban-daban, ciki har da Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo, da kuma Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu a gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Haka kuma, ya kasance mataimakin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023.

Shugaba Tinubu ya yabawa Gwamna Yusuf kan wannan naɗi, yana mai cewa hakan zai ƙarfafa haɗin kai da ake matuƙar buƙata a cikin jam’iyyar APC a Jihar Kano, kamar yadda wata sanarwa daga fadarsa ta nuna.

Ya buƙaci duk masu ruwa da tsaki su mara wa Gwamnan da mataimakinsa baya, tare da ba su cikakken goyon baya da haɗin kai.

Haka kuma ya buƙaci Murtala Garo ya yi aiki tuƙuru tare da Gwamnan domin samar da shugabanci da zai bunkasa ci-gaban jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata