Jam’iyyar APC mai mulki ta sake fuskantar koma baya a Majalisar Wakilai bayan wasu ‘yan majalisa uku sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar zuwa jam’iyyun PRP da ADC, yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara zafafa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya karanta wasiƙun sauya sheƙar a zauren majalisar, yayin zaman majalisar na ranar Laraba, kwana guda bayan majalisar ta dawo daga hutun Sallah.
A cikin wasiƙarsa, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Jama’are/Itas-Gadau ta jihar Bauchi, Rabilu Bala, wanda ya fice daga APC zuwa jam’iyyar PRP, ya ce sabanin ra’ayi da rikice-rikicen cikin gida a APC ne suka sa ya ɗauki matakin, bayan tuntubar masu ruwa da tsaki a mazaɓarsa.
Haka kuma, ɗan majalisar mai wakiltar Yola ta Arewa/Yola ta Kudu/Girei a jihar Adamawa, Abubakar Zango, ya sanar da ficewarsa daga APC zuwa jam’iyyar ADC bisa abin da ya kira muradin ƙasa da kuma abin da lamirinsa ya nuna masa, yana mai alƙawarin ci gaba da wakiltar al’ummarsa yadda ya kamata.
A wata makamancin haka, ɗan majalisar mai wakiltar Dukku/Nafada a jihar Gombe, Abdullahi, shi ma ya sauya sheƙa daga APC zuwa ADC.
Sauya shekar tasu na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan ƙawancen jam’iyyun adawa da kuma sake fasalin siyasa gabanin zaɓen 2027.
