DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabarai‘Yan sanda sun yi kame bayan gano masana’antar ƙera bindigogi a Yobe

‘Yan sanda sun yi kame bayan gano masana’antar ƙera bindigogi a Yobe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta gano wata haramtacciyar masana’antar ƙera bindigogi a garin Potiskum, tare da kama mutum bakwai da ake zargi da hannu a aikin ƙera makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Kakakin rundunar a jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce nasarar ta samu ne a wani samame da rundunar ta kai bayan samun sahihan bayanan sirri kan wasu maƙera da ke ƙera bindigogin gargajiya da sauran makamai a asirce.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar 2 ga Yuni, 2026, da misalin ƙarfe 6:00 na yamma.

Jami’an rundunar yankin Potiskum tare da haɗin gwiwar ofishin ’yan sanda na yankin sun kai samame wani wurin aikin maƙera da ke Tasha Adua a kan titin Danchuwa bayan samun rahoton ƙera haramtattun makamai a wurin.

A yayin samamen, jami’an tsaro sun kama mutum bakwai tare da ƙwace wasu kayayyaki da suka haɗa da bindigogi da aka ƙera, bututun bindiga guda 24, ƙugiyoyin bindiga guda tara, tsofaffin bindigogin gargajiya guda huɗu marasa aiki, injin goge ƙarfe guda ɗaya da kuma adda guda ɗaya.

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano sauran waɗanda ke da hannu a lamarin, masu sayen makaman da kuma manufar amfani da su. Haka kuma ana ƙoƙarin gano ko akwai wasu wuraren ƙera makamai ba bisa ƙa’ida ba a yankin.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Yobe, CP Usman Kanfani Jibrin, ya umarci jami’an bincike su zurfafa bincike domin tantance irin barazanar tsaro da irin waɗannan ayyuka ke haifarwa ga al’umma.

Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da kada su bari a yi amfani da gidajensu ko wuraren aikinsu wajen gudanar da haramtattun ayyuka, tare da buƙatar mazauna yankunan su riƙa kai rahoton duk wani motsi ko wani abu mai tayar da hankali ga hukumomin tsaro.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata