DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiLegas ta kama mabarata 45 ciki har da yara tara

Legas ta kama mabarata 45 ciki har da yara tara

Gwamnatin Jihar Legas ta kama mabarata 45, ciki har da yara tara, a wani samame da ta gudanar a yankunan Oshodi, Agege da CMS domin tsaftace muhalli da hana bara a tituna.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa na jihar, Tokunbo Wahab, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba.

Yace daga cikin mutanen da aka kama, akwai manya da matasa 22 da aka cafke a yankunan Oshodi da Agege. Haka kuma an kama manya 14 da yara tara a yankin CMS yayin wani samame na daban.

A cewar Wahab, gwamnatin jihar na ci gaba da gudanar da irin waɗannan ayyuka a wasu sassan Legas, ciki har da Admiralty Way da ke Lekki da kuma Addo Road a Ajah, domin tabbatar da tsafta da bin dokokin muhalli.

“Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Legas na yaƙi da ayyukan da take ganin suna lalata muhalli da tsarin birane” in ji shi.

A baya, gwamnatin ta bayyana cewa ta kama mutum 10,634 a cikin shekara guda bisa laifuka daban-daban da suka haɗa da tsallaka manyan tituna ba bisa ƙa’ida ba, sayar da kaya a kan titi, gurbata muhalli da kuma tura keken ɗaukar kaya a wuraren da aka haramta.

Gwamnatin ta ce daga cikin waɗanda aka kama a shekarar da ta gabata, mutum 5,715 an kama su ne saboda tsallaka manyan hanyoyi ba bisa ƙa’ida ba, yayin da wasu 3,886 suka fuskanci zargin kasuwanci kan titi da sauran laifukan muhalli.

Haka kuma an kama mutum 102 kan bayan gida a fili da kuma wasu 931 kan laifukan da suka shafi sarrafa shara.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata