A wata sanarwa da Fabrizio Romano ya wallafa, mai horas da ‘yan wasan kungiyar Real Madrid, Álvaro Arbelola, ya tabbatar da cewa zai bar ƙungiyar daga mako mai zuwa.
Arbeloa ya bayyana cewa ‘yan wasan da ya yi aiki da su sun taimaka masa wajen zama mutum mafi nagarta tare da sanya shi jin daɗin aikinsa a kungiyar.
Tsohon ɗan wasan na Spain ya kuma bayyana fatan komawa ƙungiyar a nan gaba, yana mai cewa bai bar kungiyar na har abada ba.
Arbeloa ya kuma yi magana kan yiwuwar zuwan José Mourinho, inda ya ce fitaccen kocin yana da ƙwararrun ma’aikata da yake aiki da su.
Ya bayyana cewa idan Mourinho ya dawo Madrid, zai zo ne tare da nasa tawagar masu horaswa kamar yadda ya saba yi a duk inda yake aiki.
