DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiProf Usman Yusuf ya shigar da ƙorafi ga hukumomin DSS da ’yan...

Prof Usman Yusuf ya shigar da ƙorafi ga hukumomin DSS da ’yan sanda kan Kwankwaso

Tsohon shugaban hukumar kula da inshorar lafiya ta Nijeriya NHIA, Farfesa Usman Yusuf, ya shigar da ƙorafi ga Rundunar ’yan sandan Nijeriya da hukumar tsaron ciki ta DSS, inda ya zargi Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da yin kalaman barazana da tayar da hankali a kansa.

A cikin sanarwar da ya fitar a Juma’ar nan, Farfesa Yusuf ya ce kalaman sun biyo bayan sharhin da ya yi a kafafen yaɗa labarai kan haɗakar siyasa da kuma batutuwan siyasar ƙasa. Ya bayyana cewa duk da cewa Sanata Kwankwaso bai ambaci sunansa kai tsaye ba, bayanan da ya yi sun sa mutane da dama suka fahimci cewa shi ake nufi.

Farfesa Yusuf ya kuma yi zargin cewa Sanata Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayan Kwankwasiyya su “tarwatsa” mutumin da yake magana a kansa ta amfani da kalmar “fata-fata,” wadda ya ce na iya zama kira ga tashin hankali ko tsoratarwa.

Ya ce irin waɗannan kalamai na iya jefa rayuwarsa da ta iyalinsa cikin haɗari idan aka yi la’akari da yanayin siyasar Nijeriya.

Ƙorafin ya buƙaci hukumomin tsaro su gayyaci Sanata Kwankwaso domin amsa tambayoyi tare da ɗaukar matakan kariya ga Farfesa Yusuf da waɗanda ke tare da shi.

Haka kuma ya yi kira ga shugabannin siyasa su guji kalaman da ka iya tunzura magoya baya ko kawo cikas ga zaman lafiya.

Sanarwar ta ce an aika kwafen ƙorafin zuwa Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (NSA), Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Ƙasa (NHRC), da kuma ofisoshin jakadancin Amurka da Tarayyar Turai da ke Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata