Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi maraba da matakin da Gwamnatin Nijeriya ta ɗauka na dakatar da shirin ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO, yana mai cewa matakin nasara ce ga iyaye, ɗalibai da sauran ‘yan kasa da suka nuna adawa da shirin.
Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce dakatar da shirin ya tabbatar da sahihancin gargadin da ya yi tun farko cewa ƙara kuɗin jarabawar zai ƙara jefa iyalai cikin mawuyacin hali tare da hana yara masu hazaka amma marasa ƙarfi damar ci gaba da karatu.
Ya ce duk da cewa ya yi maraba da matakin gwamnatin, abin tambaya shi ne me ya sa gwamnatin ke jira sai jama’a sun yi bore kafin ta gyara manufofin da bai kamata a ƙirƙiro su ba tun farko.
A cewarsa, shugabanci ba wurin gwaji ba ne, yana mai cewa gwamnati mai nagarta tana tuntubar masu ruwa da tsaki kafin ta yanke hukunci, ba bayan ta jefa jama’a cikin damuwa da rashin tabbas ba.
Atiku ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da manufofi ba tare da samun shawarwari ba, sannan daga baya ta janye su bayan fuskantar matsin lambar jama’a, yana mai cewa hakan alama ce ta gazawar tsara manufofi yadda ya kamata.
Ya ƙara da cewa aikin gwamnati shi ne ta yi hasashen illolin manufofinta kafin aiwatar da su, ba wai ta jira jama’a sun nuna ƙin amincewa kafin ta fahimci kuskurenta ba.
Atiku ya bayyana cewa ƙarin kuɗin rajistar WAEC da NECO zai ƙara ɗora wa iyalan Nijeriya nauyi, musamman a daidai lokacin da ake fama da hauhawar farashin kayayyaki, tsadar sufuri, ƙarin kuɗin wutar lantarki da kuma raguwar ƙarfin tattalin arziƙin al’umma.
Atiku ya yabawa iyaye, malamai, ƙungiyoyin ƙwadago, ƙungiyoyin ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki da suka haɗa kai wajen nuna adawa da shirin, yana mai cewa dimokuraɗiyya tana ƙara ƙarfi ne idan jama’a suna ɗora gwamnati kan turbar gaskiya.
Sai dai ya ce dakatar da shirin bai kamata ya zama ƙarshen batun ba, inda ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta shiga tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki domin samar da tsarin da zai tabbatar da ɗorewar gudanar da WAEC da NECO ba tare da ɗora wa iyaye ƙarin nauyi ba.
A ƙarshe, Atiku ya buƙaci gwamnatin Tinubu ta daina fito da manufofin da ke cutar da jama’a kafin ta fara sauraron ra’ayinsu, yana mai cewa tuntuba ita ce ginshiƙin shugabanci nagari.
