Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da buƙatar Najeriya ta karɓi bakuncin bikin bayar da kyaututtukan ƙwallon ƙafa na Afrika CAF na shekarar 2026 tare da babban taron ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Afrika karo na 48.
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata.
Sanarwar ta ce amincewar ta biyo bayan wata ganawa da shugaban ƙungiyar CAF, Patrice Motsepe ya yi da Tinubu a yayin taron Africa Forward Summit da ake gudanarwa a Nairobi na ƙasar Kenya.
A wajen ganawar akwai Ministar Harkokin wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu; shugaban NFF, Ibrahim Gusau; tsohon shugaban NFF kuma mai bai wa shugaban CAF shawara, Amaju Pinnick; da mukaddashin babban sakataren CAF, Samson Adamu.
Sanarwar ta ce babban taron CAF karo na 48 zai gudana a watan Oktoban bana, inda shugabannin hukumomin ƙwallon ƙafa daga ƙasashe 54 na Afrika da sauran manyan jami’an ƙwallon ƙafa za su hallara.
Haka kuma, bikin bayar da kyaututtukan CAF na daga cikin manyan bukukuwan ƙwallon ƙafa a Afrika da ke karrama fitattun ‘yan wasa da jami’ai na nahiyar.
Bikin kyaututtukan CAF na baya-bayan nan ya gudana ne a birnin Rabat na ƙasar Morocco a ranar 19 ga Nuwamban 2025.
A wajen bikin, ɗan wasan Morocco, Achraf Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika bayan taimaka wa Paris Saint-Germain ta lashe gasar UEFA Champions League da Ligue 1.
Ya zama ɗan Morocco na farko da ya lashe kyautar tun bayan Mustapha Hadji a shekarar 1998.
Morocco ta kuma samu wasu manyan lambobin yabo, inda Yassine Bounou ya lashe kyautar gwarzon mai tsaron gida, Othmane Maamma ya zama matashin ɗan wasa na shekara, sannan Ghizlane Chebbak ta lashe kyautar gwarzuwa bayan bajintarta a gasar mata ta Afrika ta 2025.
Sai dai Najeriya ta ci gaba da taka rawa a ɓangaren mata, inda mai tsaron gidan Super Falcons, Chiamaka Nnadozie, ta sake lashe kyautar gwarzon mai tsaron gida, yayin da tawagar mata ta Najeriya ta zama ƙungiyar ƙasa mafi kyau ta shekara.
Najeriya ta taɓa karɓar bakuncin bikin CAF sau huɗu a baya, inda birnin Lagos ya karɓi bakuncin na ƙarshe a watan Janairun 2015.
A wancan lokacin, tsohon ɗan wasan Ivory Coast, Yaya Touré, ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika karo na huɗu a jere, lamarin da ya daidaita tarihin Samuel Eto’o.
Haka kuma bikin na 2015 ya kasance farkon shaharar Asisat Oshoala a fagen ƙwallon ƙafar mata ta Afrika, inda ta lashe kyautar gwarzuwa ta farko a gida kafin daga baya ta kafa tarihin lashe kyautar har sau shida.
