Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tuntubi Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan batun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC da amincewar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Sunusi Bature ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce batun sauya shekar na daga cikin tattaunawar siyasa da ake yi a bayan fage gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
A cewarsa, Kwankwaso da tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, suna sane da shirin kuma suna goyon bayansa.
Ya kuma yi zargin cewa Kwankwaso na aiki ne a fakaice domin taimakawa Shugaba Tinubu wajen sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027.
