DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiNDLEA ta kama ‘yan Mexico da miyagun ƙwayoyi na sama da Naira...

NDLEA ta kama ‘yan Mexico da miyagun ƙwayoyi na sama da Naira biliyan 480

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya (NDLEA), ta ce ta kama ‘yan wata ƙungiyar da ke ƙera miyagun ƙwayoyi da ta haɗa ‘yan Nijeriya da ‘yan ƙasar Mexico, tare da kama mutane 10 da kuma kwace miyagun ƙwayoyi da sinadarai na sama da naira biliyan 480.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Abuja ranar Laraba.

Marwa ya ce jami’an sashen ayyuka na musamman na hukumar sun gano tare da rufe wani katafaren ɓoyayyen wajen sarrafa methamphetamine mafi girma da aka taɓa gani a Nijeriya.

A cewarsa, an gano wurin ne a wani daji da ke Abidagba a ƙaramar hukumar Ijebu East ta jihar Ogun bayan watanni ana tattara bayanan sirri kan ayyukan ƙungiyar.

Ya bayyana cewa jami’an NDLEA sun gudanar da sumame a jihohin Ogun da Lagos cikin sa’o’i 48, inda suka kama mutane bakwai a wurin sarrafa miyagun ƙwayoyin ciki har da ‘yan ƙasar Mexico uku da ‘yan Nijeriya huɗu.

An bayyana sunayen ‘yan Mexico ɗin da aka kama da Martinez Felix Nemecto mai shekaru 46, Jesus López Valles mai shekaru 40 da Torrero Juan Carlos mai shekaru 51.

Haka kuma an kama ‘yan Nijeriya da suka haɗa da Nwankwo Sunday Christian, Igwe Abuchi Remijus, Ifeanyichukwu Chibuike Joshua da Egwuonwu Uchenna Victor yayin da ake zargin suna sarrafa haramtattun sinadarai.

Marwa ya ce wata tawagar jami’an ta kuma kai samame gidan wanda ake zargin shugaban ƙungiyar ne, Anochili Innocent, a Golf Estate da ke Lakowe a jihar Lagos inda aka cafke shi tare da kwato fasfo da wayoyin hannu na ‘yan Mexico ɗin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata