DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeLabaraiDan majalisar Borno ya fashe da kuka yana neman goyon bayan wa’adi...

Dan majalisar Borno ya fashe da kuka yana neman goyon bayan wa’adi na biyar

Dan majalisar dokokin Jihar Borno mai wakiltar mazabar Magumeri, Honarabul Audu Mustapha Ganga, ya fashe da kuka yayin da yake roƙon al’ummarsa su mara masa baya domin sake tsayawa takara karo na biyar.

Rahotanni sun ce ɗan majalisar, wanda ya shafe shekara 16 yana wakiltar mazabar, ya yi roƙon ne bayan wasu masu ruwa da tsaki sun fara neman sabon wakilci a yankin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, Ganga ya ce duk da cewa ya fito daga gidan talakawa, ya yi ayyuka da dama ga al’ummarsa.

Ya ce, “Kun san na fito daga gida mai talauci, amma na yi muku abubuwa da dama. Ina alƙawarin ba ku kyakkyawan wakilci idan aka sake ba ni dama.”

Rahotanni sun kuma nuna cewa mutane shida sun riga sun sayi fom ɗin neman takarar kujerarsa.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata