DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Nijeriya ta haramta amfani da “Dr” ga masu digirin girmamawa

Gwamnatin Nijeriya ta haramta amfani da “Dr” ga masu digirin girmamawa

Gwamnatin Tarayya ta haramta wa masu digirin girmamawa amfani da lakabin “Dr” a gaban sunayensu a hukumance ko wajen aiki da harkokin ilimi.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya bayyana hakan ranar Laraba a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja yayin bayani kan wasu matakan da Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da su.

Gwamnatin ta ce duk wanda ya gabatar da digirin girmamawa tamkar cikakken digirin ilimi, za a ɗauki hakan a matsayin damfarar ilimi da za ta iya jawo hukunci da ɓata suna.

Alausa ya ce sabon tsarin zai kawo ƙarshen yadda jami’o’i ke bai wa mutane digirin girmamawa saboda siyasa ko kuɗi maimakon cancanta.

Ya ce, “Masu digirin girmamawa ba za su ƙara sanya ‘Dr’ a gaban sunayensu ba. Maimakon haka, za su rubuta cikakken nau’in digirin a ƙarshen suna.”

Ministan ya bayar da misalai kamar “Chief Louis Clark, D.Lit. (Honoris Causa)” ko “Mrs Miriam Adamu, LL.D. Hons.”

Sabon tsarin ya kuma takaita nau’o’in digirin girmamawa da jami’o’in Nijeriya za su bayar zuwa guda huɗu kacal, ciki har da Doctor of Laws (LL.D) da Doctor of Science (D.Sc).

Hakazalika, gwamnati ta hana jami’o’in da ba su da shirye-shiryen bayar da digirin PhD bayar da digirin girmamawa.

Alausa ya ce Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) za su sa ido wajen tabbatar da bin wannan doka.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata