Wasu masu neman takarar kujerun majalisar dokoki a jam’iyyar APC a Jihar Katsina sun sayi fom ɗin takara domin nuna rashin amincewarsu da tsarin sasanci da jam’iyyar ta amince da shi gabanin zaɓen 2027.
Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, jam’iyyar APC a jihar ta yanke shawarar fitar da ‘yan takararta ta hanyar maslaha, inda aka kafa kwamitin da tsohon gwamna Aminu Bello Masari ke jagoranta.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin ‘yan majalisar wakilai da sanatoci ba su samu tikitin sulhu ba, lamarin da ya jawo zarge-zargen cewa ana fifita ‘ya’yan manyan mutane a cikin tsarin.
Daga cikin waɗanda aka ce sun samu tikitin akwai Yusuf Buhari, ɗan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari; Muhammadu Daha, ɗan Sarkin Daura; da Abba Mangal, ɗan attajiri Dahiru Mangal.
Sai dai wasu ‘yan takara sun dage cewa dole ne a gudanar da zaɓen fidda gwani. Tsohon kwamishina a Legas, Ahmad Kabir, ya ce babu wanda ya tattauna da shi kafin a ba wani tikitin Sanatan Katsina ta Arewa.
Haka kuma, mawaƙin APC Dauda Rarara ya soki tsarin bayan an bar abokinsa Yusuf Jika a wajen tikitin Bakori/Danja.
A mazabar Daura/Sandamu/Mai’adua kuwa, Auwal Daura, ɗan tsohon shugaban DSS Lawal Daura, ya sayi fom domin kalubalantar tikitin da aka bai wa Yusuf Buhari.
Ya ce, “Maslaha dole ta kasance da yardar kowa kafin ta zama ingantacciya. Ban janye wa kowa ba saboda jama’a na goyon bayana.”
