DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeKasuwanciFarashin kayan abinci a Yulin 2026, mako na 28

Farashin kayan abinci a Yulin 2026, mako na 28

Binciken DCL Hausa kan farashin kayan abinci a wasu manyan kasuwannin Nijeriya ya nuna cewa an samu sauye-sauye a wannan mako.

Yayin da farashin wasu kayan ya sauka a wasu jihohi, wasu kuma sun ƙaru ko kuma suka ci gaba da kasancewa yadda suke a makon da ya gabata.

Ga jadawalin yadda farashin yake:

🟡 SHINKAFAR HAUSA (Tsabar Shinkafa)

Kasuwa Mako na baya Mako na yanzu Bambanci
Giwa (Kaduna) ₦115,000 ₦100,000 – ₦115,000 🟢 Saukar farashi
Dawanau (Kano) ₦120,000 ₦120,000
Dandume (Katsina) ₦106,000 – ₦117,000
Mai’adua (Katsina) ₦100,000 – ₦105,000 ₦100,000 🟢 -₦5,000 (mafi girma)
Saminaka (Kaduna) ₦100,000 ₦102,000 🔴 +₦2,000
Zamani (Adamawa) ₦102,000 ₦102,000
Mile 12 (Legas) ₦115,000 ₦115,000

🟡 SHINKAFA TA WAJE (Foreign Rice)

Kasuwa Mako na baya Mako na yanzu Bambanci
Giwa (Kaduna) ₦75,000 ₦75,000
Zamani (Adamawa) ₦70,000 ₦70,000
Dandume (Katsina) ₦70,000 ₦70,000
Mile 12 (Legas) ₦60,000 ₦65,000 🔴 +₦5,000
Dawanau (Kano) ₦63,000 ₦60,000 🟢 -₦3,000

🟡 MASARA

Kasuwa Mako na baya Mako na yanzu Bambanci
Mile 12 (Legas) ₦45,000 ₦43,000 🟢 -₦2,000
Zamani (Adamawa) ₦40,000 ₦40,000
Mai’adua (Katsina) ₦37,000 – ₦38,000 ₦37,000 🟢 -₦1,000 (mafi girma)
Dandume (Katsina) ₦30,500 – ₦32,500

🟡 WAKE

Kasuwa Mako na baya Mako na yanzu Bambanci
Mile 12 (Legas) ₦125,000 ₦120,000 🟢 -₦5,000
Giwa (Kaduna) ₦95,000 – ₦105,000 ₦95,000 – ₦105,000
Dandume (Katsina) ₦100,000 – ₦105,000
Saminaka (Kaduna) ₦100,000 ₦100,000
Mai’adua (Katsina) ₦100,000 ₦100,000
Dawanau (Kano) ₦90,000 ₦95,000 – ₦100,000 🔴 +₦5,000 zuwa ₦10,000
Zamani (Adamawa) ₦95,000 – ₦100,000 ₦90,000 – ₦95,000 🟢 -₦5,000

🟡 TALIYA (Spaghetti)

Kasuwa Mako na baya Mako na yanzu Bambanci
Dandume (Katsina) ₦18,000 ₦18,000
Mile 12 (Legas) ₦16,000 ₦16,000
Mai’adua (Katsina) ₦14,000 ₦15,000 🔴 +₦1,000
Zamani (Adamawa) ₦13,500 ₦13,500
Dawanau (Kano) ₦13,500 ₦13,500
Giwa (Kaduna) ₦12,000 ₦12,000
Saminaka (Kaduna) ₦12,500 ₦12,500

Abubuwan lura a wannan mako:

  • Masara ta ci gaba da sauka a kasuwar Mile 12 (Legas) da Mai’adua (Katsina), yayin da farashinta bai canza ba a Zamani (Adamawa).
  • Wake ya sauka da ₦5,000 a Mile 12 (Legas) da Zamani (Adamawa), amma ya ƙaru a Dawanau (Kano).
  • Shinkafa ta waje (Foreign Rice) ta ƙaru da ₦5,000 a Mile 12 (Legas), yayin da ta ragu da ₦3,000 a Dawanau (Kano).
  • Tsabar shinkafa ta ƙaru da ₦2,000 a Saminaka (Kaduna), amma ta tsaya yadda take a yawancin sauran kasuwanni.
  • Taliya ta ƙaru da ₦1,000 a Mai’adua (Katsina), yayin da farashinta bai canza ba a sauran kasuwannin da aka bibiya.
  • Dawanau (Kano) har yanzu ce ke da shinkafar Hausa mafi tsada, inda ake sayar da buhun Jamila kan ₦120,000.
  • Wake ya fi tsada a Mile 12 (Legas), duk da cewa farashinsa ya sauka zuwa ₦120,000 a wannan mako.
  • A mafi yawan kasuwannin da aka bibiya, ba a samu gagarumin sauyi ba, lamarin da ke nuna cewa farashin kayan abinci na ci gaba da kasancewa cikin yanayi mai ɗan kwanciyar hankali idan aka kwatanta da makonnin baya.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata