Gwamnatin jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen gudanar da auren-gata ga mutum 300 da suka haɗa da Musulmi da Kiristoci daga sassan jihar, wanda za a gudanar a ranar 27 ga Yuli, 2026.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa za a gudanar da shirin ne tare da haɗin gwiwar gidauniyar Nafisa Nasir Charity Development Foundation (NANAS), inda aka zaɓi ma’auratan daga ƙananan hukumomi 21 na jihar.
Shugaban kwamitin shirya shirin, Alhaji Suleiman Argungu, ya ce an zaɓi mutane ne daga cikin marayu, zawarawa da waɗanda aka raba aurensu bayan sun cika dukkan sharuɗɗan addini da na doka.
Ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku da gwamnatin jihar ke gudanar da irin wannan shiri, bayan nasarar da aka samu a shekarun 2024 da 2025.
Argungu ya ce Gwamna Nasir Idris ya amince da biyan sadaki ga dukkan amaren 300, inda za a biya N250,000 ga kowace amarya.
Ya ƙara da cewa gwamnati da abokan hulɗarta za su kuma bai wa sabbin ma’auratan kayan ɗaki, kayan abinci da sauran kayan amfanin gida domin taimaka musu wajen fara rayuwar aure cikin kwanciyar hankali.
A cewarsa, dukkan ma’auratan sun gudanar da gwaje-gwajen lafiya da suka haɗa da na ciki, genotype, HIV/AIDS, da sauran gwaje-gwajen da doka ta tanada kafin ɗaura aure.
