Akalla fasinjoji tara ne suka rasa rayukansu bayan da wasu ’yan bindiga suka bude wa wata motar haya wuta a Dungus Junction, da ke cikin al’ummar Kuru, ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Plateau.
Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne lokacin da direban motar ya tsaya a tashar domin sauke wasu daga cikin fasinjojin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa motar, wadda ke kan hanyar zuwa Jos, ta kasance cike da gawarwakin wadanda lamarin ya rutsa da su, yayin da harsasai suka ratsa sassan motar.
Lawan Suleiman, wanda makwabci ne kuma malamin ɗaya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce an kai harin ne yayin da motar ke tsaye a mahadar.
Ya ce: “Direban mai suna Ibrahim, ɗalibina ne. Uku daga cikin wadanda abin ya shafa ‘yan wannan al’ummar tamu ne da ke Bukuru. An ajiye gawarwakinsu a asibiti, amma ’yan uwansu na shirin zuwa ɗaukar su domin yi musu jana’iza.”
Shi ma kakakin ƙungiyar Berom Youth Moulders (BYM), Rwang Tengwong, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wadanda aka kashe fasinjoji ne da ke tafiya zuwa Jos lokacin da maharan suka bude wa motarsu wuta.
Ya ce: “Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:40 na dare. Dukkan wadanda aka kashe fasinjoji ne da ke tafiya zuwa Jos lokacin da ’yan bindigar suka hari motar. Daga cikin wadanda aka kashe akwai wani mamba na Operation Rainbow. Wannan lamari ne mai matuƙar bakin ciki, kuma muna alhinin asarar rayukan da aka yi.”
A cewarsa, wasu daga cikin fasinjojin sun samu raunukan harbin bindiga, kuma an garzaya da su asibitoci domin ba su kulawar gaggawa, inda daga baya wasu daga cikinsu suka mutu.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Jihar Plateau ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
