DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeBabban Labari Gwamnatin Katsina ta haramta sayar da Fetur a jarka a wasu kananan...

Gwamnatin Katsina ta haramta sayar da Fetur a jarka a wasu kananan hukumomin jihar

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da sabbin matakan tsaro domin dakile ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar.

Bayan wani taron gaggawa da jami’an tsaro da sarakunan gargajiya suka halarta, gwamnatin jihar ta fitar da sabon umarnin, wanda ya ƙunshi matakai da suka kunshi, haramta saye, sayarwa, jigilar kaya da adana man fetur a cikin jarkoki a faɗin jihar.

Rufe dukkan cibiyoyin POS da wuraren cajin waya na kasuwanci a ƙananan hukumomin Matazu, da Musawa.

Sa’annan kuma an haramta amfani da babura gaba ɗaya a waɗannan ƙananan hukumomi biyu.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an ɗauki waɗannan matakai ne domin hana isar da fetur da sauran tallafin da ke taimaka wa ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ke buya a dazuka da sauran wurare masu nisa.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Gwamna Radda ya ce rahotannin sirri na tsaro sun nuna cewa wasu cibiyoyin POS da wuraren cajin waya na taimakawa masu aikata laifuka wajen gudanar da harkokinsu da sadarwa.

Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wanda ya karya waɗannan dokoki zai fuskanci hukunci mai tsauri.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata