Ɗan wasan baya na ƙungiyar Real Madrid, Antonio Rüdiger, ya sabunta kwantiraginsa da ƙungiyar har zuwa ranar 30 ga Yunin 2027.
Rüdiger mai shekaru 33 ya koma Real Madrid ne daga Chelsea FC a shekarar 2022 bayan ya taka leda a ƙungiyoyin VfB Stuttgart da AS Roma.
Jaridar Punch ta tattaro tun bayan zuwansa Madrid, ya taimaka wa ƙungiyar lashe kofin gasar La Liga a 2024, da UEFA Champions League a 2024, da Copa del Rey a 2023.
A wani yunƙuri na farfaɗo da ƙungiyar bayan rashin manyan kofuna na tsawon kaka biyu a jere, shugaban kulob ɗin, Florentino Pérez, ya naɗa José Mourinho a matsayin sabon mai horaswa a farkon watan Yuni.
Haka kuma, Real Madrid ta sanar da ɗaukar ɗan wasan baya na Spain, Marc Cucurella, daga Chelsea, yayin da rahotanni ke alaƙanta kulob ɗin da sayen Bernardo Silva da Denzel Dumfries.
Bugu da ƙari, ana sa ran ɗan bayan Liverpool FC, Ibrahima Konaté, zai koma Real Madrid bayan karewar kwantiraginsa a Anfield.
Sabon kwantiragin Rüdiger na nuni da yadda Real Madrid ke ci gaba da gina ƙungiya mai ƙarfi domin dawo da martabarta a gasa ta cikin gida da nahiyar Turai.
