DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, July 8, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tinubu ta ce 'yan Nijeriya 150,000 na samun horon sana’o’i

Gwamnatin Tinubu ta ce ‘yan Nijeriya 150,000 na samun horon sana’o’i

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada kudirinta na amfani da tsarin Ilimin fasaha da horon sana’o’i wajen rage rashin aikin yi da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.

Gidan talabijin na TVC ya rawaito cewa akalla ‘yan Nijeriya 150,000 ne a halin yanzu ke samun horo a fannoni daban-daban na sana’o’i da fasahohi a karkashin shirye-shiryen da aka tanada domin samar da damar dogaro da kai ga matasa.

Hakan na kunshe ne a cikin kokarin gwamnatin tarayya na samar da kwararrun ma’aikata masu kwarewa da za su iya biyan bukatun da taimakawa wajen habaka masana’antu.

Gwamnatin ta bayyana cewa shirin TVET yana bai wa matasa damar koyon sana’o’in zamani da suka hada da fasahar kere-kere, aikin lantarki, walda, gyaran motoci da sauran sana’o’in da ake bukata a kasuwa.

Ta kuma ce shirin zai taimaka wajen rage yawan marasa aikin yi tare da karfafa gwiwar matasa wajen kafa sana’o’insu maimakon dogaro da aikin gwamnati kawai.

Bugu da kari, gwamnati ta bayyana cewa tana hada gwiwa da cibiyoyin horo da masu zaman kansu domin fadada shirin zuwa sassa daban-daban na kasar nan.

An bayyana cewa shirin na daga cikin dabarun gwamnatin tarayya na inganta rayuwar matasa da samar da ci gaba mai dorewa ta hanyar ilimi da koyon sana’o’i.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga matasa da su yi anfani da damar da ake samarwa domin samun kwarewa da za ta taimaka musu wajen gina makomarsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata