DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tinubu ta gaza koyon darasi daga kura-kuranta ba baya - Atiku 

Gwamnatin Tinubu ta gaza koyon darasi daga kura-kuranta ba baya – Atiku 

Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar, ya soki yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da harkokin tsaro, yana mai cewa ta kasa koyon darasi daga hare-haren da suka gabata domin inganta dabarun yaki da ta’addanci a Nijeriya.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Atiku ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane suna ci gaba da sauya dabarunsu yayin da gwamnati ke kasa sabunta nata tsare-tsaren yaki da su.

Atiku ya ce yaduwar ayyukan ta’addanci, fashi da makami da garkuwa da mutane daga yankunan Arewa zuwa sauran sassan Nijeriya na nuna cewa tsarin tsaron kasar ya gaza sauyawa saboda barazanar tsaro da ake fuskanta.

A cewarsa, hare-hare da dama da suka faru tun daga sace daliban makarantar Chibok, zuwa sabbin hare-hare a wasu sassan kasar sun nuna cewa ana ci gaba da maimaita kura-kuran baya ba tare da daukar matakan da suka dace ba.

Atiku ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sake nazarin manufofin yaki da ta’addanci na kasa, yana mai cewa ya kamata a gina sabbin dabarun tsaro bisa darussan da aka koya daga abubuwan da suka faru a baya.

Ya kuma ba da shawarar kafa gina wata hanya ta musamman da za ta hada shugabannin al’umma, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin tattara darussan da aka koya daga hare-haren baya tare da amfani da su wajen tsara sabbin manufofin tsaro.

Haka kuma, Atiku ya bukaci a kafa cibiyoyin hada bayanan sirri a kowace shiyya ta Nijeriya guda shida domin karfafa hadin gwiwa tsakanin sojoji, ’yan sanda, jami’an tsaro da kungiyoyin sa-kai wajen musayar bayanai cikin gaggawa.

Ya kara da cewa matsalar tsaro ba ta tsaya ga bangaren soja kadai ba, domin talauci, rashin aikin yi, jahilci da gazawar shugabanci suna taimakawa wajen jawo matasa shiga ayyukan ta’addanci da sauran laifuka.

Atiku ya kuma nuna damuwa kan makudan kudaden da ake warewa bangaren tsaro duk shekara, yana mai cewa duk da haka ’yan Nijeriya na ci gaba da fuskantar matsananciyar rashin tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata