Jigo a jam’iyyar ADC, Kenneth Okonkwo, ya bayyana cewa duk wanda ya kada kuri’arsa ga Peter Obi a zaben shugaban kasa na shekarar 2027, a zahiri yana taimaka wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen sake lashe zabe.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Okonkwo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Symfoni TV, inda ya ce dole ne jam’iyyun adawa su hade karkashin inuwa guda idan har suna son kayar da Tinubu a zaben 2027.
A cewarsa, rarrabuwar kawuna tsakanin jam’iyyun adawa za ta kara wa jam’iyyar APC karfi, domin rabuwar kuri’un masu adawa ita ce hanya mafi sauki da za ta bai wa Tinubu damar sake cin zabe.
Okonkwo ya zargi Obi da janyewa daga tattaunawar hadakar ADC saboda rashin son shiga zaben fidda gwani, yana mai cewa jagoran siyasa da ke son shugabantar kasa bai kamata ya guji kalubalen siyasa ba.
Ya ce babu wanda ya tilasta wa Obi shiga ADC, don haka ya kamata ya kasance cikin tsarin jam’iyyar har zuwa lokacin gudanar da zaben fidda gwani domin gwada farin jininsa a tsakanin masu ruwa da tsaki.
Tsohon kakakin jam’iyyar Labour Party ya kuma yi ikirarin cewa Sanatan Anambra ta Kudu, Victor Umeh, ya taba bayyana masa cewa hanya mafi dacewa da yankin Kudu maso Gabas zai iya samun shugabancin kasa ita ce ta hanyar kulla kawance da shugabannin Arewa.
A cewar Okonkwo, Umeh ya ce ya taba ba Obi shawarar ya amince da shiga irin wannan hadaka ta siyasa, amma ya yi zargin cewa Obi ba ya saurin karbar irin wadannan shawarwari.
Ya kara da cewa masu goyon bayan jam’iyyun adawa su yi taka-tsantsan wajen zaben da za su yi a 2027, domin a ganinsa duk kuri’ar da za a bai wa Obi za ta rage karfin hadakar adawa tare da karfafa damar Tinubu na samun wa’adi na biyu.
