Gwamnatin Nigeria ta fara shirin samar da wutar lantarki ta musamman ga rukunin masana’antu a fadin ƙasar, inda ake sa ran aikin na samar da megawatt 50 zai bai wa masana’antun da ke yankin masana’antu na Idu da ke Abuja wuta ta tsawon sa’o’i 24 a rana.
Minista a ma’aikatar kula da Masana’antu Owan Enoh ne ya bayyana hakan yayin bikin aza harsashin aikin samar da wutar a Abuja.
Ya ce samar da ingantacciyar wutar lantarki na da matukar muhimmanci wajen rage kudin samar da kayayyaki, bunkasa masana’antun cikin gida da kuma samar da ayyukan yi.
Enoh ya ce shirin na daga cikin dabarun gwamnati na bunkasa masana’antu, wadanda suka hada da karfafa samar da kayayyaki a cikin gida, kara darajar albarkatun kasa, habaka tattalin arziki da kuma kara hada masana’antun Nijeriya da kasuwannin duniya.
Ministan ya ce samar da kayayyaki a cikin gida zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasa, sa’annan gwamnati na kokarin samar da tsarin da za a iya amfani da shi a sauran rukunin masana’antu.
Enoh ya jaddada cewa farfado da masana’antun Nijeriya ba abu ne da za a cimma cikin gaggawa ba, sai da hadin gwiwa mai dorewa tsakanin gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu da al’ummomin da za su amfana da ayyukan, domin kare kayayyakin more rayuwa da tabbatar da cimma manufofin tattalin arziki.
Manajan Daraktan kamfanin Welbeck Electricity Distribution Limited, Afolabi Aiyela ya ce aikin zai fara ne da samar da megawatt 10 daga wani wuri da ke kusa da bututun iskar gas na AKK a Zuba.
Aiyela ya ce za a rarraba wutar zuwa yankin masana’antun Idu ta hanyar layin wutar lantarki mai karfin 33kV, yayin da za a samar da sauran megawatt 40 a cikin yankin masana’antun bayan an tsawaita bututun iskar gas zuwa yankin.
Ya ce a halin yanzu yankin masana’antun na Idu na da bukatar wutar lantarki da ka iya kaiwa tsakanin megawatt 300 zuwa 400, lamarin da ke nuna irin girman bukatar wutar da masana’antun yankin ke da shi.
