Kwamishinan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Neja (NSIEC), Barista Ahmed Mohammed, na ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa da mutane watanni tara bayan sace shi.
An sace Ahmed ne a ranar 29 ga Satumbar 2025 a kan hanyar Mokwa zuwa Ibbi, a Ƙaramar Hukumar Borgu, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Minna domin wani aiki na gwamnati.
Lamarin ya faru ne kusan wata guda kafin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi na jihar da aka yi a ranar 1 ga Nuwamban 2025.
Wani ɗan uwansa ya shaida wa Daily Trust cewa iyalansa sun biya naira miliyan 40 domin a sake shi, amma har yanzu masu garkuwar ba su sake shi ba.
Majiyar ta ce masu garkuwar sun sake neman ƙarin naira miliyan 300 kafin su amince da sakin sa.
A cewarsa, masu garkuwar na ci gaba da kiran iyalan kusan kullum domin matsa musu su biya sabon kuɗin fansar, amma iyalan sun ce ba su da ikon tara wannan kuɗi.
Iyalan sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Neja da hukumomin tsaro da su gaggauta shiga lamarin domin ceto Ahmed, suna mai cewa an sace shi ne yayin da yake gudanar da aikin gwamnati.
Shi ma wani aminin Ahmed, Ayuba Abubakar, ya ce iyalan sun yi duk mai yiwuwa domin ganin an sake shi, amma ba su yi nasara ba.
Ya kuma bayyana damuwa kan rahotannin da ke nuna cewa lafiyar Barista Ahmed na ci gaba da tabarbarewa a hannun masu garkuwar, tare da roƙon gwamnati da jami’an tsaro su gaggauta ɗaukar matakin da zai tabbatar da sakinsa cikin koshin lafiya.
