DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiKofa a bude take ga Kiristoci masu bukatar shiga shirin auren gata...

Kofa a bude take ga Kiristoci masu bukatar shiga shirin auren gata – Gwamnatin Kano

Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Mujahideen Aminuddeen, ya ce shirin auren gata na gwamnatin jihar a buɗe yake ga Musulmi da Kiristoci masu sha’awar shiga.

Aminuddeen ya bayyana haka ne yayin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN), inda ya ce Kiristoci ma na da damar cin gajiyar shirin.

Ya ce a shirin auren gata da aka gudanar a watan Oktoban 2023, ma’aurata Kirista uku sun shiga cikin waɗanda aka ɗaura wa aure.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da shirye-shiryen sabon zagayen auren, sai dai har yanzu ba a tabbatar ko akwai ma’aurata Kirista da suka nuna sha’awar shiga ba.

A cewarsa, shirin wanda yanzu ake kira “Auren Gata” ya shafi zawarawa, mazajen da matansu suka rasu, waɗanda aka saka, ’yan mata da samari masu neman aure.

Ya bayyana cewa manufar shirin ita ce ƙarfafa zaman lafiya a gidaje, rage lalacewar tarbiyya da kuma taimaka wa marasa galihu su yi aure cikin sauƙi.

Aminuddeen ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware naira biliyan 1.5 domin aurar da ma’aurata 1,500, inda kowanne ango zai samu naira 100,000 a matsayin sadaki, yayin da kowacce amarya za ta samu naira 100,000 domin fara sana’a.

Ya ce gwamnati za ta kuma samar wa ma’auratan kayan ɗaki, katifu da kayan abinci, tare da tabbatar da cewa an yi musu gwajin lafiya, sun dace da juna kuma angwaye na da hanyar samun abin masarufi da muhalli mai kyau.

Masana da wasu mazauna Kano sun yabawa shirin, suna masu cewa zai taimaka wajen rage talauci, ƙarfafa zaman iyali, rage saki da kuma ba matasa damar kauce wa ayyukan da suka saɓa wa ɗabi’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata