DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeSiyasaIna da yaƙinin yin tazarce a zaɓen da ake gudanarwa - Adeleke

Ina da yaƙinin yin tazarce a zaɓen da ake gudanarwa – Adeleke

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya kada kuri’arsa a zaben gwamnan jihar da ake gudanarwa a yau, Asabar, inda ya bayyana kwarin gwiwar samun nasara.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Adeleke, wanda ke neman wa’adi na biyu, ya kada kuri’arsa ne a rumfar zaɓe ta Sagba Abogunde Ward 2, Unit 9, da ke ƙaramar hukumar Ede North.

Gwamnan ya isa rumfar zaɓen da misalin ƙarfe 8:32 na safe, tare da rakiyar dimbin magoya bayansa.

Bayan kada kuri’ar, Adeleke ya bayyana damuwarsa kan wani zargin shirin kawo cikas ga gudanar da zaɓen da kuma hana wasu masu zaɓe gudanar da aikinsu na zaɓar shugabanni.

Ya yi zargin cewa an kawo wani jami’in ɗan sanda mai suna “London” daga Fatakwal zuwa jihar Osun domin kawo cikas ga zaɓe, musamman a garinsu na Ede.

Adeleke ya yi kira ga Sufeto-Janar na ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan wannan zargi tare da ɗaukar matakin da ya dace.

Haka kuma, gwamnan ya yi zargin cewa akwai wani shiri na kauce wa tsarin tattara sakamakon zaɓe da aka tanada, inda ake son a tsallake matakan tattara sakamako daga rumfa zuwa gunduma sannan zuwa ƙaramar hukuma.

Ya ce bai kamata a yi hakan ba, yana mai jaddada cewa dole ne a bi ƙa’idojin da aka tanada wajen tattara sakamakon zaɓe.

Duk da zarge-zargen da ya bayyana, Adeleke ya ce yana da cikakken yaƙinin cewa zai yi nasara a zaɓen.

“Na san, da yardar Allah, zan lashe wannan zaɓe,” in ji Adeleke.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata