Hukumar zaben Nijeriya INEC ta sanar da cewa ta yi wa ’yan Nijeriya 1,565,873 rajistar katin zaɓe cikin makonni bakwai a mataki na uku na shirin ci gaba da rajistar masu zaɓe.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin rahoton da ta fitar ranar Talata a Abuja, inda ta ce alkaluman sun haɗa da mutane 620,933 da suka kammala rajista ta yanar gizo, yayin da 944,940 suka kammala rajista ta hanyar zuwa cibiyoyin rajista a faɗin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya ruwaito.
INEC ta bayyana cewa waɗannan farko-farko ne, domin za a gudanar da tantance bayanai tare da karɓar ƙorafe-ƙorafe kafin a yi amfani da tsarin tantance bayanan masu rajista ta hanyar na’urar Automated Biometric Identification System (ABIS).
A cewar hukumar, Jihar Kano ce ta fi kowace jiha yawan sabbin masu rajista da mutum 118,207, wanda ya kai kashi 7.55 cikin ɗari na jimillar masu rajista a ƙasar.
Bayan Kano, jihar Legas ce ta zo ta biyu da mutum 78,360, yayin da Jihar Delta ta zo ta uku da mutum 76,395.
INEC ta kuma bayyana cewa an dakatar da rajistar masu zaɓe na ɗan lokaci a jihohin Ekiti da Osun, sakamakon zaɓen gwamna da aka kammala a Ekiti da kuma wanda ake shirin gudanarwa a Osun, kamar yadda dokar zaɓe ta shekarar 2022 ta tanada.
Hukumar ta ce mata sun fi maza yawan sabbin masu rajista, inda mata 821,276 suka yi rajista, wanda ya kai kashi 52.45 cikin ɗari, yayin da maza 744,597 suka yi rajista, daidai da kashi 47.55 cikin ɗari.
Rahoton ya kuma nuna cewa matasa masu shekaru 18 zuwa 34 ne suka fi yawan yin rajista, inda suka kai kimanin 1,082,985, wanda ya kai kusan kashi 69.16 cikin ɗari na jimillar masu rajistar.
Haka kuma, ɗalibai ne suka fi kowanne rukuni yawan yin rajista da mutum 384,093, sai masu sana’o’i da kasuwanci 333,539, yayin da manoma da masu kamun kifi suka kai 273,627.
Bugu da ƙari, INEC ta ce mutum 18,919 masu buƙata ta musamman (PWDs) sun yi rajistar katin zaɓe a wannan lokaci.
A ƙarshe, hukumar ta buƙaci dukkan ’yan Nijeriya da suka cancanci yin zaɓe amma ba su yi rajista ba da su yi amfani da shafinta na yanar gizo ko kuma su ziyarci cibiyoyin rajista da ke faɗin ƙasar domin samun damar kaɗa ƙuri’arsu a zaɓuka masu zuwa.
