DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeBabban Labari Jam'iyyar APC ta musanta janye sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu na...

Jam’iyyar APC ta musanta janye sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu na 2027

Jam’iyyar APC ta musanta rahotannin da ke cewa ta janye jerin sunayen mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na shekarar 2027 domin sake dubawa.

Jaridar Punch ta ruwaito sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Felix Morka, ya bayyana rahotannin a matsayin jita-jita, yana mai cewa idan akwai wani sauyi ko sabunta jerin sunayen, jam’iyyar za ta sanar da hakan a hukumance.

APC ta bayyana kwamitin ne a ranar Asabar, inda Tinubu zai jagorance shi a matsayin shugaba, yayin da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, za su kasance mataimakan shugabanni.

An kuma naɗa tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, a matsayin darakta janar na kwamitin, yayin da gwamnan Imo, Hope Uzodimma, zai zama sakatare.

Jerin sunayen da aka fitar ya haifar da ce-ce-ku-ce saboda yadda aka saka wasu manyan jami’an gwamnati da kuma wasu mutanen da ke fuskantar zarge-zargen cin hanci a gaban hukumar EFCC.

Hakazalika, wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar sun nuna rashin jin daɗi kan yadda aka cire sunayensu, duk da irin gudunmawarda suka bayar wajen yaƙin neman zaɓen da ya gabatana shekarar 2023.

Sai dai Morka ya jaddada cewa babu wani shirin janye jerin sunayen a halin yanzu, yana mai cewa duk wani sauyi da za a yi za a sanar da shi yadda ya kamata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata