DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeSiyasaJigo a jam'iyyar ADC ya bukaci dattawan arewa su fifita adalci a...

Jigo a jam’iyyar ADC ya bukaci dattawan arewa su fifita adalci a batun El-Rufa’i fiye da saɓanin siyasa

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ADC a yankin Arewa maso Yamma, Malam Ja’afar Ibrahim Sani, ya yi kira ga dattawan Arewa da shugabannin siyasa su kauce wa saɓanin ra’ayi tare da tabbatar da adalci da bin ƙa’idojin doka a halin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ke ciki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi a wata sanarwa da ya fitar yana cewa halin da El-Rufai ke ciki ya kamata ya sanya shugabannin Arewa yin nazari kan irin al’adun siyasar da ake gina wa ƙarni masu zuwa.

Ya ce siyasa na ƙara zama harkar anfani kawai, inda wasu ke nuna aminci da goyon baya idan akwai abin da za su amfana da shi, amma su juya baya ga abokan siyasarsu lokacin da suka shiga cikin matsala.

A cewarsa, ko da yake mutane na iya samun mabambantan ra’ayoyi game da El-Rufai, ba za a iya musanta irin tasirin da ya yi a rayuwar siyasa da ayyukan gwamnati a Nijeriya ba.

Sani ya nuna damuwa kan abin da ya bayyana a matsayin ƙarancin goyon bayan wasu daga cikin mutanen da suka kasance na kusa da tsohon gwamnan a baya, yana mai cewa lokacin ƙalubale ne ainihin lokacin da ya kamata aminci ya bayyana.

Ya buƙaci dattawan Arewa, masu ruwa da tsaki da shugabannin siyasa kada su bari saɓanin siyasa ya zama dalilin watsi da adalci da bin ƙa’idojin doka. Ya ce dole ne a fifita adalci a duk wani mataki da za a ɗauka kan lamarin El-Rufai, ba tare da la’akari da alaƙar siyasa ko ta kashin kai ba.

A cewarsa, idan aka tabbatar da adalci, sakamakon shari’a ya kamata ya kasance bisa abin da doka da kotuna suka tanada, ciki har da sakin El-Rufai bisa doka idan yanayi ya dace.

Da yake magana kan wasu kalaman El-Rufai da suka shafi dattawan Arewa, Sani ya ce tsohon gwamnan bai taɓa nufin cewa yankin Arewa ba shi da dattawa, malamai, sarakunan gargajiya ko gogaggun shugabanni ba.

Ya ce abin da Arewa ke bukata shi ne ingantacciyar rayuwa, wadata ga al’ummarta da makoma mai kyau ga ‘ya’yanta, yana mai jaddada cewa cimma hakan na bukatar yin nazari na gaskiya tare da ɗaukar matakan da suka dace.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata