DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasa'Kamfe ba zai kawo cikas ga ayyukan majalisa ba'

‘Kamfe ba zai kawo cikas ga ayyukan majalisa ba’

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa kamfen da shirye-shiryen zaɓen 2027 ba za su kawo cikas ga ayyukan majalisar dokokin ƙasar ba.

Akpabio ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin da yake magana da manema labarai a filin jirgin sama na Victor Attah da ke Uyo, kamar yadda mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Jackson Udom, ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Akpabio ya ce ’yan majalisar tarayya za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na kundin tsarin mulki, duk da ƙara tsananta harkokin siyasa da tuntuɓar jama’a gabanin zaɓen 2027.

Ya ce ’yan majalisar za su iya daidaita ayyukan siyasa da na majalisa, inda ya bayyana cewa za a iya gudanar da kamfen da rana ko da yamma, yayin da ake gudanar da ayyukan majalisa da safe.

Akpabio ya ce, “An zaɓe mu na tsawon shekaru huɗu, kuma za mu yi aiki na tsawon shekaru huɗu. Babu abin da zai shafi yin dokoki. Za mu ci gaba da yin dokokin da za su biya bukatun jama’a.”

Kalaman shugaban majalisar dattawan na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa da masu neman takara ke ƙara tuntuɓar jama’a da shirye-shiryen neman goyon baya gabanin babban zaɓen 2027.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata