DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeWasanniMourinho ya soki tsarin ba da kyautar Ballon d’Or

Mourinho ya soki tsarin ba da kyautar Ballon d’Or

Kocin Real Madrid, José Mourinho, ya soki tsarin da ake amfani da shi wajen zaɓen wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or, yana mai cewa bai kamata a bai wa ɗan wasa kyautar saboda kawai ya lashe gasar zakarun Turai ko Kofin Duniya ba.

Mourinho ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai kafin wasan Real Madrid da Málaga na gasar La Liga, inda ya ce kyautar ya kamata ta kasance ga ɗan wasan da tasirinsa a ƙwallon ƙafa zai ci gaba da tunawa da shi ko da ya yi ritaya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Mourinho ya ce akwai ’yan wasa kaɗan da suka bar tarihi na musamman a ƙwallon ƙafa, yana misalta da Maradona, Ronaldinho, Ronaldo, Cristiano Ronaldo, Messi, Zizou da Lothar Matthäus.

“Ba za ka bai wa ɗan wasa Ballon d’Or kawai saboda ya lashe Champions League ko Kofin Duniya ba,” in ji Mourinho.

Ya ce idan ana son a ba da muhimmanci ga lashe manyan kofuna, to ya kamata a ba da wata kyauta ga koci ko ƙungiyar da ta yi nasara, domin kyautar ɗan wasa mafi kyau a duniya abu ne na daban.

Mourinho ya kuma ce mafi kyawun ɗan wasa a duniya ba dole ne ya kasance daga Paris Saint-Germain ko ƙungiyar ƙasar Spain ba, yana mai cewa akwai ’yan wasa biyu zuwa huɗu da suka cancanci wannan matsayi.

Kocin na Portugal ya kuma yi zargin cewa wasu abubuwan siyasa na iya yin tasiri wajen zaɓen wanda zai lashe Ballon d’Or, yana mai cewa ba ya son kyautar idan siyasa ta shiga cikin lamarin.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata