DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, May 15, 2026
HomeLabaraiKotu ta umarci DSS ta saki matashiyar nan Walida, ta mika jami’inta...

Kotu ta umarci DSS ta saki matashiyar nan Walida, ta mika jami’inta ga ‘yan sanda don bincike

Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Dutse, Jihar Jigawa, ta umarci Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS da ta saki matashiyar nan ‘yar jihar, Walida Abdulhadi, ba tare da wani sharadi ba, tare da mika jami’inta, Ifeanyi Onyewuenyi, ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ana zargin jami’in DSS din ne ya sace Walida Abdulhadi mai shekaru 16, ‘yar Hadejia, tare da lalata da ita tun a shekarar 2023.

Rahotanni sun ce yarinyar ta haifi diya mace yayin da take hannun wanda ake zargi, lamarin da ya ja hankalin jama’a a ciki da wajen jihar Jigawa tun bayan da aka bayyana batun.

Kotun ta dage yanke hukunci kan lamarin zuwa ranar Litinin, 26 ga watan Maris, bayan sauraron hujjojin bangaren masu kara da kuma lauyoyin da ke kare wadanda ake kara.

Yayin da yake yanke hukunci a ranar Talata, Mai shari’a Hassan Dikko ya umarci hukumar DSS da ta saki yarinyar ba tare da wani sharadi ba.

Har ila yau, ya umurci hukumar da ta fito da Onyewuenyi tare da mika shi ga rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa domin gudanar da cikakken bincike.

A cikin hukuncin nasa, Mai shari’a Dikko ya soki hukumar DSS bisa zargin boye jami’inta da ake tuhuma da aikata wannan mummunan laifi.

Kotun ta kuma soke duk wani bincike da DSS ta ce tana yi kan jami’in nata.

Mai shari’ar ya bayyana cewa DSS ba ta da hurumin doka na bincikar jami’inta a irin wannan lamari bisa dokar National Security Agency Act da ta kafa ta.

Ya kara da cewa, boyewa da kare jami’in da ake zargi da aikata wannan laifi mai muni abin Allah wadai ne.

Ya jaddada cewa ‘yan sanda da kotuna ne kadai ke da ikon gudanar da bincike da shari’a kan irin wadannan tuhume-tuhume.

Haka kuma, ya bukaci ‘yan sanda su dauki matakin gaggawa da zarar an mika jami’in domin tabbatar da gaskiya da kuma saurin gudanar da bincike.

Kokarin da Punch ta yi na jin ta bakin lauyan DSS bayan hukuncin bai yi nasara ba.

Tun da farko, Kotun Majistare ta Hadejia ta umarci DSS da ta mika Walida ga iyayenta ba tare da wani sharadi ba, tare da mika jami’in DSS din da ake zargi ga kwamishinan ‘yan sanda na jihar Jigawa domin bincike.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata