DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeLabaraiKotun ɗaukaka ƙāra ta tabbatar da rajistar jam'iyar NDC

Kotun ɗaukaka ƙāra ta tabbatar da rajistar jam’iyar NDC

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, ta soke hukuncin babbar kotun tarayya da ke Lokoja, jihar Kogi, wanda ya bayar da umarnin soke rajistar jam’iyyar ‘Nigeria Democratic Congress’ NDC a matsayin jam’iyyar siyasa.

Kotun ta yanke hukuncin ne da rinjayen kuri’u biyu da daya, inda alkalai biyu daga cikin kwamitin mutum uku suka tabbatar da amincewar hukumar zaben Nijeriya INEC da rajistar NDC, tare da bayyana hukuncin babbar kotun da aka yanke ranar 26 ga Yuli a matsayin hukunci marar inganci.

Alkalai biyu, masu shari’a Mohammed Danjuma da Muslim Sule Hassan, sun ce babbar kotun ta yi amfani da ikon da bai dace ba tare da karya tsarin kotuna, saboda ta sake zama tana duba hukuncin da ita kanta ta yanke a ranar 10 ga watan Disambar 2025, wanda ya amince da rajistar NDC da INEC ta yi.

Kotun ɗaukaka ƙarar ta kuma yi watsi da takaddamar da aka yi kan tambarin NDC, bayan wata kungiya karkashin jagorancin ‘Peace Movement Party’ PMP ta yi ikirarin cewa tambarin nata ne.

Alkalai biyun sun ce daukaka karar da NDC ta shigar tana da hujja, don haka suka amince da ita.

Sai dai mai shari’a Okon Abang, wanda shi ne alkali na uku a kwamitin ya yi adawa da hukuncin, inda ya tabbatar da hukuncin babbar kotun na soke rajistar NDC.

Ya ce bai ga wani dalilin da zai sa a soki hukuncin babbar kotun ba, domin a cewarsa, kotun ta yi aiki bisa ka’idojin adalci da bai wa kowane bangare damar kare kansa.

Mai shari’a Isah Dashen na babbar kotun tarayya da ke Lokoja ne ya soke wani hukuncin da kotun ta bayar a baya, wanda ya umarci INEC ta yi wa NDC rajista.

Hakan ya biyo bayan wata kara da PMP ta shigar, tana iƙirarin cewa ba a sanya ta cikin wadanda ake kara a shari’ar farko ba, duk da cewa tana da sha’awar shari’ar.

Babbar kotun ta amince da hujjar PMP, inda ta ce ya kamata a bai wa dukkan bangarorin da ke da ruwa da tsaki a lamarin damar shiga shari’ar kafin a ba INEC umarnin yin rajistar jam’iyyar.

Daga nan ne mai shari’a Dashen ya bayar da umarnin sake sauraron shari’ar, tare da tabbatar da cewa dukkan bangarorin da abin ya shafa za a sanya su cikin shari’ar.

NDC, wacce tuni ta tsayar da ‘yan takararta domin babban zaben 2027, ba ta amince da hukuncin ba, inda ta daukaka kara zuwa kotun ɗaukaka ƙara.

Kotun ta yi watsi da hukuncin babbar kotun, tare da tabbatar da rajistar NDC a matsayin jam’iyyar siyasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata