Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta soke hukuncin babbar kotun tarayya da ya rushe wasu daga cikin ƙa’idojin hukumar zaɓen Nijeriya INEC na gudanar da zaɓen 2027, tare da tabbatar da cewa ƙa’idojin za su ci gaba da aiki.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis, yayin da take sauraron ƙarar da INEC ta shigar kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya a shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/517/2026.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta kuma ce Jam’iyyar Youth Party wadda ta shigar da ƙarar ba ta da hurumin yin hakan, saboda ta gaza nuna yadda ƙa’idojin INEC suka cutar da ita ko mambobinta.
Kotun ta ce jam’iyyar ba ta gabatar da hujjar cewa ƙa’idojin sun haifar mata da wata illa da za ta ba ta damar shigar da ƙarar ba.
Alƙalai uku na kotun ɗaukaka ƙarar sun kuma bayyana cewa Alƙalin Babbar Kotun Tarayya, Mai Shari’a Mohammed Garba Umar, ya yi kuskure wajen soke wasu daga cikin ƙa’idojin INEC a hukuncin da ya yanke ranar 20 ga Mayu, 2026.
A wancan hukunci, Babbar Kotun Tarayya ta ce INEC ba ta da ikon tilasta wa jam’iyyun siyasa gudanar da zaɓen fidda gwani cikin wa’adin da hukumar ta kayyade.
Kotun ta kuma soke wasu sassa na jadawalin INEC da suka bukaci jam’iyyun siyasa su gabatar da kundin rajistar mambobinsu da bayanan ‘yan takararsu kafin wa’adin da dokar zaɓe ta tanada.
Sai dai INEC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin, inda ta ce Babbar Kotun Tarayya ta yi kuskure wajen fassara wasu sassa na dokar taɓe ta 2026.
Lauyan INEC, Dokta Alex Izinyon, ya yi zargin cewa kotun farko ba ta yi hukunci kan ƙorafin farko da hukumar ta gabatar ba, lamarin da ya ce ya tauye mata damar samun adalci ne.
Kotun ɗaukaka karar ta amince da ƙarar INEC tare da soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya, abin da ya dawo da ingancin ƙa’idojin INEC na shirye-shiryen zaɓen 2027.
A yayin karanta hukuncin, Mai Shari’a Okon Abang ya ce doka ta bai wa INEC ikon gudanar da zaɓe a Nijeriya, kuma kotuna ba za su tsoma baki ba matuƙar hukumar tana aiki cikin ikon da doka ta ba ta.
