DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeLabaraiKu daina tashin jarirai daga bacci - Likitoci

Ku daina tashin jarirai daga bacci – Likitoci

Ƙwararrun likitoci a fannin kula da lafiyar yara sun shawarci iyaye da su guji tashin jariran su daga barci ba tare da wani dalili da ya zama na gaggawa ba, suna gargadin cewa yawan katse musu barcin da suke yi bisa tsarin jikinsu na iya shafar ƙwaƙwalwar su da sauran matakan ci gaban jikinsu.

Masanan sun bayyana cewa, duk da cewa ba lallai ne jarirai su yi barci a lokaci ɗaya da iyayensu ba, katse musu barci domin ya dace da yadda iyaye suke yi na iya haifar musu da illa fiye da amfani.

Sun jaddada cewa barci na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasar manyan sassan jiki, musamman ƙwaƙwalwa, don haka jarirai na buƙatar isasshen barci domin samun lafiyayyen ci gaba.

Sai dai sun yi bayanin cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne jariri ya samu sa’o’in barcin da ake buƙata cikin awa 24, ba wai takamaiman lokacin da yake yin barcin ba.

Binciken da PUNCH Healthwise ta gudanar ya nuna cewa wasu iyaye kan tashi jariransu daga barcin yamma saboda suna ganin idan suka bar su suka yi dogon barci a lokacin, zai yi musu wuya su sake yin barci da dare.

Yawancin iyaye na tsoron cewa jaririn zai ƙi yin bacci har cikin dare ko kuma zuwa wayewar gari, yana kuka, wasa ko neman kulawa, yayin da sauran ‘yan gida ke ƙoƙarin yin barci.

Saboda haka, wasu iyaye kan katse barcin yammar jaririn da nufin su yi barci da wuri da dare.

Sai dai ƙwararrun likitocin yara sun yi gargadin cewa yawan katse tsarin barcin jariri na iya rage ingancin barcinsa, tare da sa ya fi wahala ya saba da tsarin barci mai kyau.

Da yake zantawa musamman da PUNCH Healthwise, wani ƙwararren likitan yara a Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Aminu Mohammad, ya ce jarirai tun daga haihuwa zuwa kusan shekaru biyu na buƙatar isasshen barci domin samun lafiyayyar rayuwa.

A cewarsa, yawanci jarirai na buƙatar yin barci tsakanin awa 12 zuwa 16 a kowace rana, yayin da sababbin jarirai ke buƙatar kusan awa 14 zuwa 16.

Ya ce isasshen barci na da matuƙar muhimmanci saboda yana taimakawa bunƙasar manyan sassan jiki, musamman ƙwaƙwalwa.

Farfesan ya bayyana cewa jarirai na dogaro ne da abin da ake kira circadian rhythm, wato tsarin halittar jiki da ke tsara lokacin farkawa da barci.

Ya ce idan aka hana yara yin barci a lokacin da jikinsu ke buƙatar hakan, akwai yiwuwar ba za su samu isasshen hutu daga baya ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata