Jigo a jam’iyyar ADC a Nijeriya, Dino Melaye, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da iyalansa su fara haɗa kayansu domin ficewa daga fadar shugaban ƙasa, yana mai ikirarin cewa jam’iyyarsa za ta kayar da APC mai mulki a babban zaɓen shekarar 2027.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Melaye ya yi wannan furuci ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise, inda ya ce ƙara gajiyar da ‘yan Nijeriya suka yi da gwamnatin Tinubu za ta bayyana a sakamakon zaɓen 2027.
Tsohon sanatan ya zargi gwamnatin Tinubu da gazawa wajen magance matsalolin yunwa, rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta. Ya ce ‘yan Nijeriya sun gaji da abin da ya kira rashin kyakkyawan shugabanci, yawan karɓo bashi da kuma gazawar aiwatar da kasafin kuɗi yadda ya kamata.
A cewarsa, duk da cewa gwamnati na karɓo bashi domin aiwatar da kasafinta, har yanzu akwai kwangilolin da aka bayar tun shekarar 2024 da ba a biya kuɗinsu ba, yana mai zargin cewa har yanzu ana ci gaba da aiwatar da kasafin shekarar 2024 a cikin 2026.
Melaye ya kuma ce matsin rayuwa, rashin tsaro, kashe-kashe da kuma zargin cin hanci sun haifar da gibi mai girma tsakanin gwamnati da al’ummar Nijeriya. Ya ce jama’a na bibiyar abubuwan da ke faruwa kuma za su bayyana matsayarsu ta hanyar ƙuri’unsu.
Ya ƙara sukar gwamnatin Tinubu, yana mai cewa a halin yanzu jama’a ne ke jin tsoron gwamnati, maimakon gwamnati ta kasance mai jin tsoron fushin jama’a da kuma kula da ra’ayinsu.
Har ila yau, jigon na ADC ya zargi shugaban ƙasa da yin kalaman da, a cewarsa, za su iya nuna cewa magudin zaɓe, tashin hankali da ƙwacen akwatunan zaɓe abubuwa ne da za a amince da su a harkokin siyasa. Yana mai cewa irin waɗannan kalamai ba su dace da shugaban ƙasa da ya kamata ya zama abin koyi ga matasan Nijeriya ba.
Melaye ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa zaɓen 2027 zai haifar da sauyin gwamnati, yana mai kira ga shugaban ƙasa da iyalansa su shirya ficewa daga fadar shugaban ƙasa.
A kalamansa, sakamakon zaɓen zai nuna cewa jama’a sun yanke hukunci kan gwamnatin mai ci, yana mai jaddada kwarin gwiwar ADC na ganin tana da damar karɓar mulkin ƙasar saboda, a cewarsa, ‘yan Nijeriya na neman sauyi.
Dino Melaye wanda ya bar jam’iyyar PDP a watan Yulin 2025 kafin ya shiga ADC a Nijeriya, ya kasance daga cikin fitattun masu bayyana ra’ayoyin jam’iyyar tare da shiga wasu matakai na shari’a da muhawarar siyasa a madadinta.
